Kara karbuwar kasuwar ranar ma’aikata na nuni ga farfadowar kasuwar yawon shakatawa ta Sin
2023-04-30 17:12:59 CMG Hausa
A yayin da ranar 1 ga watan Mayun bana, wato ranar ma'aikata ta duniya ke kara gabatowa, kasar Sin ta kaddamar da shirin bunkasa yawon shakatawa na al'adu don hutun ranar. Wuraren yawon shakatawa ma suna shirin kaddamar da jerin nau'o'in ayyuka daban-daban, wadanda suka kunshi abubuwa masu dimbin yawa, don habaka kasuwar yawon bude ido da ta al'adu, da bunkasa manyan ayyukan raya al’adun jama’a.