logo

HAUSA

Amurka Mai Matukar Son Amfani Da Karfin Tuwo Ta Zama Sanadin Tashin Hankalin Duniya

2023-04-29 21:20:32 CMG HAUSA

DAGA MINA

Abokai, a ran 24 ga watan nan ne kwamitin nazarin halin zaman lafiya na kasa da kasa dake birnin Stockholm na kasar Sweden wato SIPRI a takaice, ya gabatar da alkaluman yawan kudaden da kasashe daban-daban suka kashe wajen ayyukan soja, adadin da ya nuna cewa, a shekarar 2022, yawan kudaden ayyukan soja da Amurka ta kashe ya kai dala biliyan 877, wanda ya kai kashi 39% bisa na dukkan kudaden da kasashen duniya suka kashe a fannin, hakan ya sa Amurka ta ci gaba da kasancewa a matsayin farko a duniya a wannan fanni.

Wanzar da zaman lafiya da hadin kai, da samun bunkasuwa tare, matsaya ce ta bai daya da kasashen duniya suka cimma, to amma shin mene ne ya sa Amurka ke kashe kudade masu dimbin yawa haka a zamanin da ake rungumar zaman lafiya?

Bisa kididdigar da aka yi, Afghanstan, da Iraqi, da Libya, da Sham, da dai sauran kasashe sun nutse cikin yake-yake, saboda hujjar yaki da ta’addanci da Amurka ta yi amfani da ita a kasashen tun bayan shekarar 2001. Ban da wannan kuma, Amurka ta rura wuta ga wasu kasashe da su hambarar da gwamnatocinsu, abin da ya jefa yankuna da dama cikin tashe-tashen hankula, baya ga kuma yadda take ta karawa rikicin Rasha da Ukraine gishiri. Bisa kididdigar da SIPRI ya yi, yawan tallafin kudaden soja da Amurka ta baiwa Ukraine a shekarar 2022 ya kai dala biliyan 19.9, adadin ya kai matsayin koli da wata kasa ta baiwa wata kasa ta daban a fannin aikin soja cikin shekara daya tun bayan yakin cacar baka.

Abubuwan da suka faru sun shaida cewa, yawan kudaden ayyukan soja masu dimbin yawa da Amurka ta kashe bai kawo wa duniya zaman lafiya ba, wanda ‘yan siyasar kasar suka ikirarin tabbatarwa. A maimakon hakan, wadannan ‘yan siyasa sun haifar da tashe-tashen hankula a duniya. Idan gwamnatin Amurka ta kashe irin wadannan kudade masu yawa wajen kyautata zaman rayuwar jama’arta a cikin gida, ba shakka al’ummar kasar za su kara jin dadin zaman rayuwarsu. (Mai zane da sharhi: MINA)