logo

HAUSA

Zargin Sin Da Hannu A Ta’addanci A Nijeriya: Tuggu, Makirci Ne Da Kisisinar Turawan Yamma

2023-04-29 19:18:17 CMG Hausa

Daga Abdulrazaq Yahuza

A tsakiyar watan Afrilu ne wata jaridar da ake wallafawa a Birtaniya (The Times) ta yi wani rahoto da ya yi zargin ‘wai’ wasu Sinawa da ke aiki a Nijeriya musamman bangaren ma'adanai suna daukar nauyin ta'addanci a wasu sassa na Nijeriya domin kawai su fake da guzuma su harbi karsana.

Tun daga lokacin da jaridar ta fitar da rahoton ana ci gaba da samun martanoni daban-daban daga masharhanta masu adalci wadanda suke rabe tsaki da tsakuwa. Shi ma ofishin jakadancin Sin da ke Nijeriya ya fitar da sanarwar manema labarai a kan karyata zargin mara tushe balle makama.

Idan aka bi rahoton jaridar kan lamarin, za a tarar zargin nata ya ta'allaka ne a kan wata shadara guda daya tak, da ke cewa "shugabannin 'yan ta'adda sun bugi kirjin cewa a yanzu wuyansu ya isa yanka, hatta Sinawan da ke son aiki (hakar ma’adanai) a yankunan da suke dole su biya kudin haya." Kuma fa wannan din ma an tsinto ne a wani bidiyo da ke gararamba a shafukan sada zumunta.

Idan aka ce an ga wani abu a shafukan sada zumunta, (galibi mu a Nijeriya) ba a daukar abin da muhimmanci har sai an tabbatar da shi daga daya daga cikin shafukan sahihan gidajen jaridu ko takwarorinsu na kafafen yada labarai na lantarki. Domin akwai masu shirya bidiyo ko kirkiro da labari da nufin janyo hankulan jama'a a shafinsu (traffic) saboda taro da sisi da za su iya samu da hakan. A kan wannan, na san da yawa sun yi watsi da rahoton a matsayin zuki ta malle.

Kazalika, ni ban yi mamaki ba da na ji cewa wata jaridar Birtaniya ce ta wallafa rahoton, domin duk mai bibiyar yadda kawancen Sin da Afirka ke bunkasa ci gaba a kasashenmu, ya san da zaman Turawan Yamma ba za su kyale ba, dole za su rika hada tuggu da kisisina da makirce-makircen wargaza lamarin. Domin su sun kasa yin hakan saboda mugunta. Mu dauki misali daga mulkin mallakar da suka yi wa Afirka, tatsar yankin suka yi maimakon kawo masa ci gaba, da yawan masana tarihi sun bayyana cewa da arzikin Afirka ne aka gina Turai. Ta hanyar bautarwa ko cinikin bayi da sace-sacen ma'adanai da suka yi zuwa kasashensu.

To ma wai, me ya sa Turawan Yamma ba za su yi irin wannan bakin kishin ba, Sin ta samu karbuwa dari bisa dari a Afirka, saboda ta bude wa nahiyar kofofin bunkasa tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa. Sin ta gina layukan dogo sama da kilomita 6,000, titunan mota sama da kilomita 6,000, kusan tasoshin teku 20 da kuma manyan tashoshin wutar lantarki sama da 80 a Afirka. Bugu da kari, ta taimaka wajen gina asibitoci da dakunan shan magani sama da 130, da makarantu sama da 170, da filayen wasanni 45 da kuma aiwatar da ayyukan bunkasa noma sama da 500 duk a Afirka.

Yadda mutum zai fahimci alherin da ke cikin wadannan ayyukan shi ne, a Nijeriya, Sin ta gina katafariyar tashar tekun da babu kamarta kaf a Yammacin Afirka a Lekki da ke Jihar Legas. Ana sa rai wannan tashar, ta samar da kudi kusan Dala Biliyan 360 tare da samar da aikin yi akalla Dubu Dari da Saba'in (170,000).

Ke nan me ya sa Turawan Yamma ba za su yi hassada ba, tun da sun riga Sin zuwa nahiyar da shekaru aru-aru amma ba su tsinana komai ba sai bautarwa da sace-sacen dukiyar yankin? Hatta lokacin da suka ce sun bai wa kasashen Afirka ‘yancin cin gashin kai, ba su amince kasashen sun karbi ragamar tafiyar da tattalin arzikinsu ba sai bayan wasu shekaru da suka ga uwar-bari. Misali mu a Nijeriya, an ba mu ‘yancin kai daga Ingila a 1960, amma ragamar tafiyar da tattalin arzikin kasa bai dawo hannun shugabanninmu baki daya ba sai a 1963.

Abin da Turawan Yamma suka fi kwarewa a kai shi ne kulle-kulle da makirce-makirce a kasashen duniya. Sun fi so su ga ana gwabza yaki a tsakanin ‘yan kasa don wargaza kasa. Misalin abin da ya faru a Libiya ya isa zama shaida, sannan kwanan nan ga gobarar da suka kunna a Sudan.

Ita kuwa Sin, salonta ya bambanta, tana mutunta ‘yancin kasashen da take kawance da su, ta fi yarda da cin gajiyar juna maimakon kashin dankali, ta fi son yaukaka zumunci da inganta zaman lafiya maimakon tashin-tashina. Kokarin da Sin ta yi na sake hade kan Saudiyya da Iran a ‘yan kwanakin baya manuniya ce kan haka.

Tabbas! Lokaci ya yi da Afirka za ta kara nuna wa Turawan Yamma cewa kan mage ya waye, muna bukatar abokan ci gaba ne ba masu kawo koma-baya ba, masu mutunta ‘yancinmu ba masu tilasta mana auren jinsi da keta mana kyawawan al’adu da muka gada ba.