logo

HAUSA

Zakaran hawa tsaunuka na Sin ya kafa tarihin gudun fanfalaki

2023-04-27 16:48:34 CRI

Jin Feibao, dan wasan hawa manyan tsaunuka ne dan asalin kasar Sin, wanda ya cimma nasarar kaiwa kololuwar manyan tsaunukan dake nahiyoyin duniya baki daya, ya kuma kai ga kewaye mahadar duniya biyu, ta arewaci da kudanci wato “North Pole” da “South Pole” cikin watanni 18 da kwanaki 24. Baya ga haka, Jin ya yi nasarar kammala gudun fanfalaki guda 100 cikin kwanaki 100.

Wani abokin Jin ya bayyana a lokacin da abokin na sa ya yi nasarar kafa tarihin hawa tsauni mafi tsayi a shekarar 2007, cewa burin Jin wanda a yanzu yake da shekaru 60 a duniya, shi ne karfafawa karin mutane gwiwar shiga harkokin wasanni.

Shi kan sa Jin ya taba cewa, "Idan mutum zai iya kaiwa kololuwar tsaunin Qomolangma, to zai iya kammala gudun fanfalaki". Bayan Jin ya kammala gudun fanfalaki a karon farko a birnin Yantai na gabashin kasar Sin, sai ya kara sha’awar wasan gudu, kuma daga nan ne ya kara kaimi, har ya kai ga kammala dukkanin tseren fanfalaki guda 6 mafiya girma da ake yi a sassan duniya daban daban.

Daga nan sai ya shafe shekaru sama da 2 yana gudu a cikin tsaunuka, da hamada, da dazuka, da yankuna masu matukar sanyi, inda ya yi gudun da ya kai akalla kilomita 100 a ko wane gudun da ya yi, kuma daga karshe ya yi nasarar kafa matsayin bajimta da aka yiwa lakabi da "777 a shekarar 2018, lokacin da ya kammala gudun fanfalaki guda 7 a nahiyoyin duniya 7 cikin kwanaki 7.

Game da hakan, Jin ya ce "Idan kaiwa ga sassa 7 na nahiyoyin duniya ya zama jigon rayuwa ta, to kammala gudun fanfalaki a wadannan nahiyoyi ya alamta saurin da rayuwa ta take da shi".

Duk dai da wannan nasarori da Jin ya samu, har yanzu bai yi shirin tsayawa ba.

Kafin hakan a shekarar 2018, Jin ya kaddamar da wani shiri mai lakabin "Fairyland Marathon", wanda a karkashin sa ya kammala gudun fanfalaki 100 cikin kwanaki 100 a jere, inda ya ziyarci gasannin ta hanyoyin kauyukan lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin.

Manufar shirin dai a cewar sa ita ce yayata kyawawan wurare masu ban sha’awa. da al’adun gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni, wadanda ba na kaya ba.

Jin ya ce “Dukkanin nasarorin da na cimma sun shiga muhimmin tarihi na rayuwa ta. A rana ta farko, na isa tsaunuka masu kankara; A ta biyu na kai kwarin kogi. Idan na ji yunwa, ina da taliyar shinkafa da nake ci, sannan na sha shayin Pu'er idan na ji kishirwa. Ko da yaushe akwai ‘ya’yan itacen “plums” da “peach” da mazauna wurin da nake bi kan bani kyauta"

Sai dai duk da wannan nasara da Jin ya rika samu a kan hanyar sa ta kaiwa ga inda ya nufa, ya hadu da babban kalubale bayan isar sa saman tsaunin Jiaozi mai tarin dusar kankara, wanda shi ne tsauni mafi tsayi a lardin Yunnan.

A lokacin Jin ya gamu da matsalar matsanancin ciwon gwiwa da mahadar idon sawun sa, don haka Jin wanda a lokacin ke da shekaru 55, ya rika shan maganin kashe radadin ciwo a kullum, kafin ya kai ga daga kofin karshe na nasarar da ya samu a kwana na 100.

Game da hakan, Jin ya ce "Sauri ba shi ne matsala ta ba, babban kalubalen shi ne jurewa na ci gaba da gudu. Na cimma nasarar hakan kafin na cika shekaru 60"

Nasarar da Jin ya cimma a Yunnan, ta sanya shi gano babbar damar da yake da ita a fannin shiga gasar gudun fanfalaki ta fuskar lafiyar jiki da kuma raya al’adu. A yanzu, wannan gwarzo na kasar Sin yana shirin yin wani gudu, domin ratsa sassan yankunan kabilun kasar Sin 56, domin nunawa duniya bangarorin rayuwar su, da al’adun su, da wuraren asali masu ban sha’awa dake kasar, tare da fatan jan ra’ayin karin jama’a su  shiga gudun fanfalaki.

A cewar Jin "Kawai ka shiga wasan gudu. Za ka ga duniya ta daban, kana za ka ji sauyi a kai kan ka".