logo

HAUSA

Batun Taiwan batu ne mafi jawo hankalin al’ummar Sinawa

2023-04-26 11:24:34 CMG Hausa

Daga ranar 8 zuwa 10 ga watan Afrilu ne, rundunar PLA ta gudanar da sintiri da atisayen soja na gargadi a kewayen tsibirin Taiwan. Matakin na zama wani gargadi mai tsanani ga masu neman ’yancin kan Taiwan suke yi tare da rukunonin ketare, kuma matakin ya zama wajibi domin kare ikon mulkin kasar da cikakken yankinta.

Rahotanni na cewa, rundunar ta gudanar da wannan sintiri da atisayen soja na gargadi a zirin Taiwan da arewaci da kudanci da kuma gabashin tsibirin na Taiwan bisa shirin da aka tsara.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce ayyukan masu rajin ’yancin kan Taiwan tare da masu goya musu baya daga waje, babbar barazana ce ga zaman lafiyar zirin Taiwan.

Kamar yadda ruwa da wuta ba za su hadu wuri daya ba, haka ma burin ballewar yankin Taiwan, ya saba da burin wanzar da zaman lafiya da daidaito a zirin na Taiwan. Kuma domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan, ya zama wajibi a tabbatar da rashin amincewa da duk wani mataki na ingiza burin 'Samun ’yancin kan Taiwan".

Kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma yankin Taiwan wani yanki ne cikin kasar Sin wanda ba za a iya taba raba shi daga kasar Sin ba. kuma, gwamnatin Jamhuriyyar Jama’ar Kasar Sin, ita ce halastacciyar gwamnati daya tilo dake wakiltar kasar Sin bisa doka. Wannan shi ne muhimmin bayani game da manufar “Kasar Sin daya tak a duniya”, wanda ya samu amincewar gamayyar kasa da kasa. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)