logo

HAUSA

Bai dace a bari Okinawa ta sake zama fagen daga ba

2023-04-26 21:31:57 CMG Hausa

Da sanyin safiyar Larabar nan ne al’ummun Okinawa ta kasar Japan, suka wayi gari da ganin dandazon dakarun sojin kasar, da tarin ababen hawan su, sun cika tashoshin ruwa da tituna, a gabar da gwamnatin kasar ta ayyana shirin ta na jibge makami mai linzami samfuri na Patriot 3 a wurin.

Kafafen watsa labarai na kasar sun soki lamirin gwamnatin kasar, bisa yadda take ci gaba da fadada ayyukan ta na soji, wanda hakan ya sabawa "Yarjejeniyar zaman lafiya", tare da haifar da barazana ga tsaro da daidaito a yankin da kasar take.

Domin nuna bukatar zaman lafiya, a ranaikun 24 da 25 ga watan nan, wata tawagar kansiloli ta Okinawa, ta mika kwafin takardar cimma matsaya a fannin diflomasiyyar zaman lafiya wadda suka amincewa ga ma’aikatar tsaron kasar, da majalissar gudanarwa, da ma’aikatar harkokin wajen kasar.

Takardar ta bukaci gwamnatin Japan da ta rungumi manufofin da aka tanada, cikin kundin siyasa 4 tsakanin Sin da Japan, domin bunkasa kawancen kasashen 2.

Takardar da suka gabatar, ta kuma tuhumi gwamnatin Japan, bisa matsayar kuskure da ta dauka game da kasar Sin, wanda hakan ya zamo mataki irin sa na farko da majalissar ta su ta dauka a Japan.

Ta la’akari da bukatar bai daya ta al’ummun Okinawa su miliyan 1.46, da kuma sauran masu burin wanzar da zaman lafiya a Japan, bai dace gwamnatin kasar ta kawar da kai daga wannan bukata ba. (Saminu Alhassan)