logo

HAUSA

WHO: Masu kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro, da wadanda ke mutuwa sanadiyar cutar sun daidaita a shekarar 2021

2023-04-25 07:49:27 CMG Hausa

Hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta bayyana cewa, yawan masu kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro da kuma wadanda ke mutuwa sanadiyar cutar a duniya baki daya, ya tsaya yadda yake a shekarar 2021, sakamakon namijin kokarin da kasashen da abin ya shafa suke yi.

A cewar sabon rahoton da hukumar WHO ta fitar, an yi kiyasin cutar ta zazzabin cizon sauro ta halaka mutane dubu 619 a duniya a shekarar 2021, idan aka kwatanta da mutane dubu 625 da cutar ta halaka a shekarar 2020.

Masu kamuwa da cutar a duniya ya ci gaba da karuwa tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021, amma karuwar ba ta kai ta shekarar 2019 zuwa 2020 ba. Adadin masu fama da cutar a duniya, ya kai miliyan 247 a shekarar 2021, idan aka kwatanta da miliyan 245 a shekarar 2020 da miliyan 232 a shekarar 2019.

A cewar babban darektan hukumar lafiya ta duniya WHO Dr. Tedros

Adhanom Ghebreyesus, wannan dan karamin karuwar da aka samu, ta samo asali ne sakamakon namijin kokarin da kasashen da ke fama da cutar ke yi, domin dakile munanan illolin da cutar COVID-19 ta haifar ga ayyukan yaki da cutar ta zazzabin cizon sauro.

Kayan aiki na farko shi ne gidajen sauro masu dauke da magani. Hukumar WHO ta kuma ba da shawarar yin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro daga lokaci zuwa lokaci, a tsakanin yaran da ke zaune a yankunan da cutar ke yaduwa a wasu lokuta a kasashen Afirka.

A halin da ake ciki, rahoton ya bayyana cewa, magungunan artemisinin (ACTs) da ake amfani da su, su ne mafi tasiri wajen magance cutar mai nau’in P. falciparum. An yi kiyasin cewa, kasashe masu fama da cutar zazzabin cizon sauro a duniya, sun sayi maganin ACT da ya kai miliyan 242 a shekarar 2021, idan aka kwatanta da maganin na ACT miliyan 239 da aka saya a shekarar 2019.

A cewar rahoton, kalubaloli dai sun ci gaba da kasancewa a nahiyar Afirka, wanda ke da kusan kashi 95 na masu kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro da kuma kashi 96 na mace-mace sanadiyar cutar a duniya a shekarar 2021.