logo

HAUSA

Abdoulmajid: Ya dace a kara karfafa hadin-gwiwa tsakanin kasashen Nijar da Sin

2023-04-25 15:48:46 CMG Hausa

Abdoulmajid, dan asalin jihar Maradin Jamhuriyar Nijar ne, wanda a yanza haka yake cikin mataki na karshe na karatun digiri na biyu, a fannin kasuwancin kasa da kasa, a jami’ar Hebei dake birnin Baoding na kasar Sin.

A zantawar da yayi da Murtala Zhang, malam Abdoulmajid ya bayyana ra’ayin sa kan ci gaban kasar Sin, da hadin-gwiwar da ake yi tsakanin kasar sa wato Nijar da Sin.

A karshe, ya bayyana fatan sa ga ‘yan uwan sa mutanen Nijar. (Murtala Zhang)