Liu Shenting, manomi ne da ya gama karatu a jami'a
2023-04-25 07:57:16 CMG Hausa
Liu Shenting yana noman 'ya'yan itatuwa a lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Ya gama karatu daga wani shahararriyar jami'ar kasar Sin, inda ya samu digiri na biyu a fannin kimiyya da fasahar laturoni. Yau shekaru 7 da suka wuce, ya koma garinsa ya fara aikin gona a gona. Sakamakon aiwatar da manufofin farfado da yankunan karkara, ya sa karin masu ilmi kamar Liu Shenting, suke komawa yankunan karkara, inda suka raya garuruwansu da kyau bisa ilminsu da kwarewarsu. (Tasallah Yuan)