logo

HAUSA

Ingancin al’ummar kasa ya tabbatar da ci gaban tattalin arzikin Sin

2023-04-24 15:16:52 CMG HAUSA

 Asusun kula da yawan mutane na MDD ya yi hasashen cewa, adadin al’ummar kasar Indiya zai zarce na kasar Sin a tsakiyar bana, inda hakan zai sa Indiya ta kasance kasa mafi yawan mutane a duniya. Ganin haka ya sa wasu kafofin watsa labaru na kasashen yamma yin amfani da wannan dama wajen shafawa kasar bakin fenti, inda suka ce wai “Dalilin yawan mutane zai hana farfadowar al’ummar kasar Sin”. Amma mene ne gaskiyar lamarin?

 

Hakika bai kamata a yi hasashen ci gaban kasar Sin bisa jimlar mutanenta kadai ba, ya dace a mai da hankali kan ingancin karuwar tattalin arzikin kasar. An lura cewa, karuwar tattalin arzikin kasar Sin a rubu’in farkon bana ta kai kaso 4.5 bisa dari, lamarin da ya shaida cewa, kasar tana samun ci gaba yadda take bukata.

Kana ingancin al’ummar kasa wani bangare ne da ya kamata a lura da shi. A halin yanzu, adadin al’ummar Sinawa dake aiki ya kai kusan miliyan 900, kuma adadin yana karuwa da miliyan 15 a ko wace shekara. Ban da haka adadin Sinawa wadanda suka kai matakin digiri na farko a jami’o’i ya kai sama da miliyan 240, ko shakka babu kasar Sin tana cike da kuzari yayin da take kokarin raya tattalin arzikinta.