logo

HAUSA

Melissa: Ina so in ba da gudummawa ga bunkasar dangantaka tsakanin Rasha da Sin

2023-04-24 20:13:19 CMG Hausa

Melissa, 'yar asalin kasar Rasha, daliba ce dake a aji na biyu, na neman digiri na biyu a fannin Koyar da Sinanci, a Jami'ar Koyon Harsunan Waje ta Beijing. Duk da cewa ba ta dade a kasar Sin ba, amma tana jin Sinanci sosai. Rayuwa mai dacewa, wadataccen abinci, da al'adun Sinawa masu kayatarwa, su ne dalilan da suka sa Melissa ke fatan ci gaba da zama a kasar Sin.

Melissa tana magana da Sinanci da sauri, wanda ke nuna cewa, ta iya Sinanci sosai, amma a hakika wannan ita ce shekara ta 6 kacal da ta fara koyon Sinanci. Wannan yarinya da ta fito daga Novosibirsk, wadda ta kware sosai wajen koyon harsuna, ta shaida wa manema labarai cewa, koyon Sinanci zai kara mata damar samun ci gaba.

 “Lokacin da nake zaben fannonin da zan koya, na yi la’akari sosai da yanayin da ake ciki a yanzu haka. Ana ta karfafa dangantaka tsakanin Rasha da Sin, ko shakka babu koyon Sinanci zai yi amfani ga makoma ta.”

Tun lokacin da ta fara koyon Sinanci, Melissa ta himmatu wajen shiga cikin gasa, da ayyuka daban-daban, kamar su ayyukan da kwalejin Confucius ke shiryawa, da gasar "Gadar Sinanci" da dai sauransu. A shekarar 2020, Melissa ta lashe gasar "Gadar kasar Sin" karo na 19 a bangaren rukunin Rasha, kuma ta samu gurbin karo ilmi a kasar Sin.

A watan Satumba na shekarar 2022, bayan ta yi karatu a yanar gizo tsawon shekara guda, daga karshe Melissa ta iso kasar Sin, kuma ta isa harabar jami'ar koyon harsunan waje ta Beijing, wadda ta dade tana matukar tunanin ta.

“Yadda zaman rayuwar dalibai yake a jami’armu, ya burge ni sosai. A nan dalibai da yawa suna karatu da rana, da yamma kuma, na kan ga wasu dalibai suna rawa a dandali, wasu daliban kuma suna wasan badminton, da kwallon kwando da dai sauransu. Wannan wata hanya ce ta yin abota a wancan lokacin, kuma makarantar wuri ne da ke iya samar da yanayi mai kyau na sada zumunci. "

Bisa ga daidaituwar manufar kandagarki da shawo kan cutar COVID-19 da gwamnatin kasar Sin ta dauka, Melissa ta kuma soma fita daga harabar makaranta don yin bincike a birnin Beijing, da sauran biranen kasar Sin. Ta ce, ko da yake ta taba kallon wasan kwaikwayo ta gidan talabijin na kasar Sin, da shirye-shiryen nishadi na kasar, ta hakan ta fahimci wasu abubuwa game da halin da ake ciki a kasar Sin, amma sai da ta zo kasar Sin don yin karatu da rayuwa, ta kara fahimtar abubuwan more rayuwa da dama da suka zama ruwan dare a cikin al'ummar kasar Sin.

“Ina ganin abin da ya fi ba ni mamaki shi ne yadda ake biyan kudi ta wayar salula a nan kasar Sin, kowa na yawo da wayarsa ne kawai, ba bukatar yawo da jakar kudi. A kasar Rasha dole ne mu dauki tsabar kudi, katunan kudi, da dai sauransu. Don haka, wannan kuma wani bangare ne da ya fi gamsar da ni, ya dace sosai. "

n ta zo birnin Beijing, Melissa ta ji cewa, wannan birni ne mai saurin tafiya ta fuskokin aiki da zaman rayuwa da dai sauransu, saboda haka ta damu, cewa zai yi wuya ta saba da irin wannan hali. Amma bayan ta shiga halin zaman rayuwar na hakika, Melissa ta kaunaci wannan "saurin tafiya". Baya ga haka, kuma soyayya da abokantaka, da malamanta, da abokan karatunta suke nuna mata, sun sanya ta ji kamar tana zaune ne a gida.

“Suna abokantaka da ni sosai, ban yi tsammanin za su kasance abokai na sosai kamar haka ba. Abokai na masu yawa Sinawa suna son yin magana da mu, kuma suna yin abota da ni, musamman daliban da ke koyon Rashanci. Su kan tambaye ni yadda muka koyi Sinanci, da yadda mutanen Rasha suke rayuwa, wadanne halaye suke da su, da sauransu. "

A halin yanzu, Melissa ta riga ta samu takardar shaidar kammala karatun digiri na biyu a fannin ilimin harsuna, daga jami'ar koyon harsunan waje ta Beijing, kuma za ta yi karatun digiri na uku a kasar Sin nan da shekaru hudu masu zuwa. Har ila yau, tana fatan bayar da ta ta gudunmuwar a fannin inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, wato Rasha da Sin ta hanyar kokarinta.

“Dangantakar dake tsakanin kasashenmu biyu ta kara kusanto mu da juna, a ko da yaushe muna iya taimakawa juna, kuma muna gudanar da hadin gwiwa mai kyau yadda ya kamata, don haka ina da kyakkyawan fata kan makomarmu a nan gaba. Ko shakka babu, ina kuma so in ba da gudummawata ga ci gaban da ke tsakanin Sin da Rasha, kamar yada al'adun kasar Sin. Ta gabatar da Rasha ga Sinawa, da gabatar da Sin ga Rashawa, ina yin amfani da wannan hanya don ba da gudummawata don karfafa dangantakar dake tsakanin kasashenmu biyu. "