logo

HAUSA

Tsaro wani hakki ne na dan Adam

2023-04-24 16:56:51 CMG Hausa

Abokaina barka da karamar Sallah! Na ga wasu hotunan bukukuwan murnar Sallah da wasu abokai suka yi tare da iyalansu, ta shafukan sada zumunta. Na ji dadin yadda suke biki cikin wani yanayi na murna da kwanciyar hankali. Saboda kun san ba a ko ina ake iya yin haka ba.

Yanzu haka a kasar Sudan da ba ta da nisa da kasar Najeriya, ana ci gaba da fama da dauki ba dadi. Kana a Mali da Burkina Faso, su ma sun samu abkuwar hare-hare a kwanakin nan. Ko a wasu yankunan kasar Najeriya ma, hare-haren ’yan fashi da masu neman satar mutane na ci gaba da ci wa jama’a tuwo a kwarya.

Kowa ya sani, tsaro wani hakki ne na dan Adam, kuma tushen ci gaban al’umma. Saboda idan babu tsaro, ba za a iya rayuwa ba, balle ma a samu ci gaban sauran harkoki.

A wasu wurare, yanayi na tashin hankali ya kori masu neman zuba jari, abin da ya sa ake fuskantar rashin damar raya masana’antu, da karancin guraben aikin yi da za a iya samar wa matasa. Daga baya, matasan da ba su da aikin yi su kan fara kokarin neman duk wata hanyar samun kudi, har ma wasunsu suka fara karya doka, lamarin da ke kara lalata yanayin tsaron da ake ciki. Ta wannan hanya, wadannan wurare sun tsunduma cikin da’irar faduwa, inda yanayi na yamutsi da talauci ke kara tsananta.

Yayin da a wasu wurare, mabambantan kasashe, da rukunoni ke gwabza fada a tsakaninsu, saboda kowanensu na neman tabbatar da tsaron kai. Sai dai fadan da suke yi ya sa tsaro ya zama wani abu mai nisa, wanda kusan ba za a iya tabawa ba.

Ta la’akari da wannan yanayin da ake ciki ne, ya sa kasar Sin gabatar da shawarar tabbatar da tsaron duniya, a shekara daya da ta gabata. Babban makasudin shawarar shi ne, a yi kokarin samar da wani yanayi na tsaro na bai daya. Wato don tabbatar da tsaro a duniyarmu, ana bukatar samun tattaunawa, da hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban. Dole ne a tabbatar da tsaron kowa, ta yadda tsaron zai iya dorewa. Saboda haka, ya kamata, mabambantan kasashe su kara kokarin musayar ra’ayi da hadin kai, da nacewa ga adalci, da bin ka’idojin kasa da kasa, da neman daidaita rikici kafin ya yi tsamari, ta yadda za a iya tabbatar da tsaron daukacin bil Adama cikin hadin gwiwa.

A nata bangare, kasar Sin ta ba da wannan shawara ta tabbatar da tsaro a duniya, ita ma ta aikata hakan kamar yadda ta fada. Cikin shekarar da ta wuce, mun gane ma idanunmu yadda kasashen Saudiya, da Iran, suka kawo karshen sa-in-sa a tsakaninsu, da farfado da huldar diplomasiyya, bisa sulhun da kasar Sin ta yi, da yadda kasar Sin ta yi kokarin neman sanya kura ta lafa a kasar Ukraine, tare da gabatar da wata muhimmiyar takardar bayani, wadda a cewar Stephane Dujarric, kakakin babban magatakardan MDD, wata muhimmiyar gudunmowa ce ga yunkuruin daidaita rikicin.

Ban da haka kuma, cikin wani dogon lokacin da ya gabata, kasar Sin ta yi kokarin hadin gwiwa da kasashen Afirka, da kasashe masu tasowa na sauran sassan duniya, a bangaren aikin tsaro da ba na gargajiya ba, wanda ya hada da yaki da ta’addanci, da samar da isashen abinci, da aikin jinya, da dai sauransu. Inda kasar Sin ta tura sojojinta fiye da dubu 50 don halartar aikin wanzar da zaman lafiya da MDD take gudanarwa, da taimakawa kasashen Afirka horar da kwararru masu fasahohin aikin gona, da noman sabbin nau’ikan amfanin gona masu inganci, da samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 fiye da biliyan 2.2 ga kasashe da kungiyoyi fiye da 120, da tura dimbin tawagogin likitoci zuwa kasashe daban daban, inda suka samar da hidimar jinya ga mutane kimanin miliyan 290.

Sai dai mun san ba za a iya tabbatar da tsaron duniya ta karfin wata kasa kadai ba. Aikin na bukatar hadin gwiwar kasashe daban daban. A nan, mun gamu da katari, ganin yadda mutanen duniya ke ci gaba da daukaka zaman lafiya da bunkasuwar tattalin arziki, a wannan zamanin da muke ciki. Yanzu haka, wasu kasashe da kungiyoyi fiye da 80 sun yaba da kasar Sin, da nuna mata goyon baya, kan shawarar da ta gabatar ta tabbatar da tsaro a duniya. Hakan ya nuna cewa, kasashe daban daban sun fara cimma ra’ayi daya, wato manufar yin babakere a duniya, da ta sa hannu cikin harkokin gida na sauran kasashe, da yin takara cikin wani mummunan yanayi, da ra’ayi na son kai, kawai suna lahanta tsaro na kowa. Yayin da ra’ayin kasar Sin na tabbatar da tsaro na bai daya, ya zama wata manufa ta girmama mutunci na kowace kasa, da hakki na tushe na daidaikun mutane. (Bello Wang)