Bai Kamata Japan Ta Zuba Ruwan Da Sinadarin Nukiliya Ya Gurbata Cikin Tekun Pasifik Ba
2023-04-22 21:11:14 CMG Hausa
Ranar 22 ga wata, rana ce ta duniyarmu, wato “The World Earth Day” a Turance, kana rana ce ta doka ta duniya. Wasu kungiyoyi masu zaman kansu, da kungiyoyin kiyaye muhalli a duniya sun yi gangami, domin nuna adawa da shirin gwamnatin kasar Japan na zuba ruwan da sinadarin nukiliya ya gurbata daga Fukushima zuwa teku.
Ban da haka kuma, a kwanan baya, hukumar Greenpeace ta sossoki lamirin gwamnatin Japan kan shirin na ta, wanda ya saba wa yarjejeniyar dokokin teku ta MDD, da sauran dokokin kasa da kasa, hukumar ta kuma zargi gwamnatin Japan da gazawa wajen sauke nauyin kimanta illolin da shirinta zai haifar kan muhalli.
Cikin shekaru 2 da suka wuce, tun bayan da gwamnatin Japan ta sanar da shirin zuba ruwan da sinadarin nukiliya ya gurbata zuwa teku, ana ta bayyana adawa, da kuma nuna shakku kan shirin na Japan. Amma gwamnatin Japan din ta kau da kai, tare da yin aniyar aiwatar da shirinta, duk da cewa har yanzu, hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA, ba ta kaddamar da rahoton ta na kimanta tasirin hakan ba.
Babban taken ranar duniyarmu a bana shi ne “Zuba kudi domin duniyarmu”. A shafinta na Internet, MDD ta yi kira ga kasashen duniya da su raya tattalin arziki mai dorewa. Zuba ruwan da sinadarin nukiliya ya gurbata cikin teku, ba zai shafi Japan kadai ba, domin kuwa hakan zai shafi daukacin bil Adama ne. Har ila yau tekun Pasifik, ba wuri ne da Japan za ta zuba shara ba ne, maimakon haka, teku ne da wasu kasashe suke dogaro da shi. Don haka kamata ya yi Japan ta daidaita ruwan ta hanyar da ta dace, bisa sanin ya kamata da kuma kimiyya. Kafin dukkan sassa masu ruwa da tsaki sun tabbatar da cewa, shirin Japan ba zai haifar da illa ba, bai kamata Japan ta aiwatar da shirin na ta ba. (Tasallah Yuan)