logo

HAUSA

Me ya sa shugabannin kasa da kasa da manyan ‘yan kasuwa suka yi ta kawo ziyara kasar Sin?

2023-04-22 22:33:23 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

Daga ranar 18 zuwa 21 ga wata, shugaban kasar Gabon Ali Bango Ondimba ya kawo ziyarar aiki kasar Sin bisa gayyatar da aka yi masa, inda shugabannin kasashen biyu suka tsai da kudurin daga matsayin cikakkiyar dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, zuwa cikakkiyar dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare.

Shugaba Ali Bango ya kasance shugaba na farko daga nahiyar Afirka da kasar Sin ta karba a wannan shekara, haka kuma, yana daga cikin shugabannin kasashe da shiyyoyi da suka kawo ziyara kasar Sin cikin lokacin da bai kai wata daya ba, wato biyowa bayan ziyarar firaministocin Spaniya, da Malaysia da Singapore, da shugaban kasar Faransa, da shugabar tarayyar Turai, sai kuma shugaban kasar Brazil.

Ban da su kuma, kusan manyan jagororin kamfanonin kasa da kasa guda 100 da suka hada da Apple, da Mercedes-Benz, da makamantansu ma suka ziyarci kasar Sin, don neman damammaki na kasuwanci.

Amma me ya sa shugabannin kasa da kasa da manyan ‘yan kasuwa suka yi ta kawo ziyara kasar Sin? A yanayin da ake ciki na rashin samun kwanciyar hankali da kuma rashin tabbas, me ya sa kasashen duniya suka rika zura ido ga kasar Sin?

Domin amsa tambayoyin, za mu fara da yin nazari kan yanayin siyasar da ake ciki a duniya, inda yanzu haka ake fuskantar tashin hankali da sauye-sauye, inda kasashen yamma da ke karkashin jagorancin Amurka suka yi ta haifar da rarrabuwar kawuna, da yin fito-na-fito a tsakanin kasashen duniya, matakin da ya jawo damuwa da rashin jin dadi ga kasashe da dama. Kasar Sin a nata bangaren, tana ganin duniya ta ishi dukkanin kasashe su bunkasa kan su, kuma ta ba da shawarar kafa sabon salon dangantakar kasa da kasa mai girmama juna, da adalci, da hadin gwiwar cin moriyar juna, inda bi da bi, ta gabatar da manufar gina zaman al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, da shawarar ziri daya da hanya daya, da shawarar raya duniya, da shawarar kiyaye tsaron duniya, da kuma shawarar wayin kai ta duniya, wadanda suke kunshe da tunanin gargajiya na kasar na rungumar zaman lafiya da kiyaye bambancin juna, wadanda kuma suka samu karbuwa daga akasarin kasashen duniya.

Shugaban kasar Gabon kafin ya fara wannan ziyara ma ya yaba da wadannan shawarwari da kasar Sin ya gabatar, yana mai cewa, shawarwarin za su taimaka ga kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya, tare da tabbatar da ci gaban kasa da kasa. Shi ma shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a yayin ziyarar sa ya ce, Faransa na nacewa ga manufar diflomasiyya mai 'yanci, kuma tana ganin ya kamata Turai ta kiyaye ‘yancinta ta fannin tsare-tsarenta, har wa yau ya bayyana rashin amincewa da jawo rarrabuwar kawuna, da yin fito-na-fito a tsakanin kasa da kasa.

A fannin tattalin arzikinta kuma, tun bayan da kasar Sin ta inganta matakan kandagarkin annobar Covid-19, tattalin arzikin kasar Sin ya farfado. Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta samar da kwanan nan sun shaida cewa, a farkon watannin ukun bana, mizanin tattalin arziki na GDP na kasar ya kai yuan trilliyan 28499.7, wanda ya karu da kaso 4.5% bisa na makamancin lokacin bara, har ma hukumomin kasa da kasa da dama sun kyautata hasashensu kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar cikin wannan shekara. Kasancewarta kasa mafin karfin tattalin arziki na biyu a duniya, farfadowar tattalin arzikin kasar na amfanar duniya baki daya a maimakon ita kanta. Babbar darektar asusun ba da lamuni na duniya IMF, Kristalina Georgieva ta ce, farfadowar tattalin arzikin kasar Sin na nufin kasar Sin ka iya bayar da gudummawar da za ta kai kaso 1/3, ko ma fiye da haka ga ci gaban tattalin arzikin duniya a bana. Abu mafi muhimmanci kuma shi ne yadda kasar Sin ke nacewa ga kiyaye dunkulewar ci gaban duniya, da ma inganta bude kofarta ga ketare, ta yadda karin kasashen duniya za su ci gajiyar bunkasuwarta. Daidai da yadda Ola Källenius, shugaban darektocin kamfanin Mercedes-Benz, wanda ya kawo ziyara kasar Sin kwanan baya ya fada, cewa “za mu ci gaba da zuba jari ga kasar Sin, kasancewar yadda kasar Sin na kiyaye bunkasuwarta, da bude kofarta ga ketare, ya samar da damammaki masu daraja gare mu.”

Har kullum kasar Sin na rungumar dunkulewar duniya baki daya, kuma tana fatan ganin bunkasuwar kasa da kasa ta bai daya. Ko a tabbatar da ‘yancin kai ta fannin siyasa, ko kuma a dogara ga wasu, ko a bude wa juna kofa ta fannin tattalin arziki, ko kuma a rika yin gaba da juna, duk kasa mai hankali za ta yi zabin da ya dace.(Lubabatu)