logo

HAUSA

Me Ya Sa Karuwar Tattalin Arzikin Sin Na Watanni Uku Na Farkon Bana Ta Zarce Zaton Jama’a

2023-04-22 18:38:03 CMG Hausa

Kwanan baya, kasar Sin ta bayar da alkaluman kididdigar tattalin arzikin kasar na watanni uku na farkon shekarar da muke ciki, inda aka nuna cewa, adadin GDP na kasar a rubu’in farkon bana ya kai kudin Sin yuan biliyan 28499.7, adadin da ya karu da kaso 4.5 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara. Lamarin da ya jawo hankalin kafofin watsa labarai na kasa da kasa, inda suka ba da labaran cewa, karuwar tattalin arzikin kasar Sin a watanni uku na farkon shekarar bana ta zarce zaton jama’a, kasar Sin na samun farfadowa cikin sauri, kasar Sin ta samu ci gaban tattalin arziki a farkon shekarar da muke ciki.