logo

HAUSA

Yadda Kamfanin Huawei Na Sin Ke Fadada Moriyar Fasahar Sadarwa A Tanzania

2023-04-20 17:46:10 CMG Hausa

Sanin kowa ne cewa a zamanin yau, daya daga muhimman fannonin da ke ingiza ci gaban duniya shi ne fannin fasahar sadarwa, wanda karkashinsa, al’ummun duniya ke cin gajiyar musayar bayanai da sakwanni ta kafofi daban daban, ciki har da na wayar salula da yanar gizo ko intanet. Hakan ne ma ya sa a kasashe masu tasowa da dama, gwamnatoci ke kara azamar samar da manyan ababen more rayuwa a wannan fanni.

A ’yan shekarun baya bayan nan, kasar Sin na kara samun manyan nasarori a fannonin fasahar sadarwa ko ICT, matakin da ke kara ingiza ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummunta a dukkanin bangarori. Kuma kamfanonin kasar masu ruwa da tsaki suna kara taka rawar gani wajen fitar da fasahohinsu ga kasashen waje, ta yadda daukacin al’ummun duniya za su kai ga cin gajiya daga hakan.

Kamfanin Huawei mai gudanar da ayyukan raya fasahohin sadarwa na zamani na kasar Sin, daya ne daga manyan kamfanonin duniya da suka yi fice a wannan fage. Inda ko da a farkon makon nan ma ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar fadada turakun samar da hidimar yanar gizo a kasar Tanzania. Bayan kammalarsa, aikin wanda aka yi wa lakabi da NICTBB, zai samar da hidimar yanar gizo ga gundumomin kasar 23 dake kasar ta gabashin Afirka.

Tuni dai kamfanin na Huawei ya tabbatar da shirinsa na yin aiki tare da tsagin Tanzania, wajen ganin an cimma nasarar kafa manyan ababen more rayuwa da za su warware kalubalen da kasar ke fuskanta a fannin sadarwar yanar gizo, matakin da ko shakka babu zai bunkasa fannin fasahar sadarwa a kasar.

A bangaren gwamnatin Tanzania kuwa, manufar wannan aiki na NICTBB shi ne hade dukkanin yankunan kasar da hidimar yanar gizo. Baya ga haka, aikin zai iya taimakawa Tanzania samun damar dunkulewa ta fuskar hidimar fasahar sadarwa da kasashe makwaftanta, kamar Zambia, da Malawi, da Kenya, da Uganda, da Rwanda, da Burundi.

Lura da wannan manufa, muna iya cewa kamfanin Huawei na kasar Sin na taka rawar gani wajen bunkasa fasahar sadarwa a kasashen Afirka, yayin da kasashen nahiyar ke fafutukar samun ci gaba a wannan muhimmin fanni, mai ba da damar bunkasa tattalin arziki da kyautata jin dadin bil adama. (Saminu Hassan)