logo

HAUSA

Dan damben Boksin na Sin ya lashe kambin hukumar WBO

2023-04-20 21:15:03 CMG Hausa

Zakaran damben boksin dan kasar Sin Zhang Zhilei, ya doke takwaransa na Birtaniya Joe Joyce, a fafatawar da suka yi ranar Asabar din karshen makon jiya. Zhang ya doke Joyce a zagaye na 6, inda da karbe kambin damben hukumar WBO na ajin masu nauyi.

Da yake tsokaci game da nasarar sa, Zhang ya ce "Wannan dambe ne da ya zo min da sauki sama da yadda na yi tsammani. Na yi aiki tukuru kafin karawar amma yanzu na ci gajiyar kwazo na". Zhang wanda zai cika shekaru 40 a wata mai zuwa, ya bar sansanin horon sa dake Amurka zuwa filin wasan dambe na Copper Box Arena dake birnin Landan, inda dubban ‘yan kallo suka rika shewa da murnar ganin karawar sa da Joyce mai shekaru 37. Yanzu haka dai Zhang ya yi nasara a wasanni 15 a jere.

Kafin fara fafatawar, magoya bayan Joyce sun rika daga murya suna jinjina masa, amma duk da haka, ya sha kaye tun daga zagayen farko na karawar, inda ya rika shan naushi daga Zhang, har zuwa zagaye na 6, inda Zhang din ya samu nasara a kan sa.

Joyce wanda ke rike da lambar azurfa ta gasar Olympic da aka gudanar a birnin Rio na Brazil a shekarar 2016, ya rika tangadi yayin da yake shan naushi daga Zhang, kuma jini ya rika fita daga fuskarsa, har zuwa lokacin da alkalin damben ya tsayar da wasan a zagaye na 6, ya kuma baiwa Zhang nasara. Yanzu haka dai Zhang din ya maye gurbin Joyce, a matsayin wanda zai yi takara da zakaran dambe ajin masu nauyi na duniya karkashin hukumar Boksin ta WBO, wato Oleksandr Usyk dan asalin kasar Ukraine.

Zhang ya ce "Ina godewa mai horas da ni, da ‘yan tawaga ta, da masu mara min baya daga Sin, wadanda suka jira har tsakar dare domin su kalli wasa na. Wannan tamkar kyautar bikin ranar haihuwa ta ne mafi daraja, daga ‘yan tawaga ta da ni kai na".

Duk da nasarar da ya samu, a yanzu Zhang na fatan cimma nasarar lashe kambin duniya, ya kuma bayyana cewa, ba shi da niyyar hutawa mai tsawo, har sai ya kai ga cimma burin sa na lashe babban kambin na duniya baki daya.


An yi bikin “Yin wasanni masu tsafta”

A ranar Juma’ar makon jiya ne kasar Sin ta gudanar da bikin “Yin wasanni masu tsafta”, bikin da ke wayar da kan al’ummar duniya game da bukatar gudanar da dukkanin harkokin wasanni bisa kiyaye dokokin shan magungunan kara kuzari.

Hukumar kasa da kasa mai yaki da shan magungunan kara kuzarin ‘yan wasa ko WADA, ita ce ta kebe wannan rana tun a shekarar 2014, inda ake yin bikin ta a duk watan Afirilu, da nufin fadakar da ‘yan wasan motsa jiki na duniya, da jami’an dake taimakawa ‘yan wasan, da masu shiga harkokin wasa, da hukumomin shirya wasanni, da ma masu yaki da shan kwayoyin kara kuzari a wasanni.

A bana, taken bikin shi ne "Wasa daya kungiya ta gaskiya", kuma wannan shekara ta 2023, bikin ya mayar da hankali ne ga fadakarwa ga mahalarta wasanni, ta yadda za su ba da goyon baya da yin aiki tare, domin tsaftace wasanni daga shan kwayoyin kara kuzari.

Kaza lika a bana, kamar a shekarun baya, hukumar yaki da shan magungunan kara kuzarin ‘yan wasa ta kasar Sin, ta yi kira ga ‘yan wasan kasar, da tawagogin su, da magoya baya, su rika bayyana halin da suka shiga, da tunanin su game da yadda za a tsaftace wasanni daga wannan matsala ta hanyar amfani da yanar gizo, karkashin jigon bikin, wato “Yin wasanni masu tsafta”, inda ake sa ran su rika dora hotuna da bidiyo, ko shirye shiryen ilmantar da jama’a, kan illar amfani da magungunan kara kuzarin ‘yan wasa.


Adadin wadanda suka mika takardun shiga jarrabawar dillanci ‘yan wasan kwallo ga hukumar FIFA sun kai sama da 6,000

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta ce ta karbi takardun masu fatan shiga jarrabawar samun shaidar dillancin ‘yan wasan kwallon kafa da yawan su ya kai 6,586 daga sassan kasa da kasa dake da rajista da hukumar har 138.

Jarrabawar dai ita ce irinta ta farko da FIFAn ta gudanar, tun bayan fara aiwatar da dokar ba da shaida ga masu aikin dillancin ‘yan wasa ko (FFAR), a watan Janairun bana.

Wata sanarwa da FIFA ta fitar ta bayyana cewa, "Fara aiwatar da tsarin ba da lasisi ga dillanan ‘yan wasa, muhimmin jigo ne a dokar FFAR, domin kuwa hakan zai daga matsayin kwarewa, da da’ar aiki ta samu dillancin ‘yan wasa, kuma hakan zai haifar da karuwar ingancin hidimomin da ‘yan wasa za su rika samu daga dillalan su.

Da yake karin haske game da hakan, babban mashawarcin FIFA a fannin shari’a da kiyaye doka Emilio Garcia Silvero, ya ce kaso mai yawa na masu shiga jarrabawar sun samu tabbacin amincewa da bukatar su daga FIFA, wanda hakan ke nuna yadda masu sha’awar wannan sana’a daga sassa daban daban na duniya ke fatan yin aiki karkashin sabuwar dokar, wadda za ta tabbatar da ana kare ingancin hidimomi a fannin dillancin ‘yan wasa, karkashin dokokin da aka tsara.

Baya ga jarrabawar da aka tsara gudanarwa a watan nan na Afirilu, FIFA ta kuma tsara gudanar da wata jarrabawar a ranar 20 ga watan Satumba, da wasu a watannin Mayu da Nuwamban shekarar 2024.


FIFA ta kaddamar da shirin horas da ‘yan wasa game da warware takaddamar shari’a mai nasaba da wasanni

Hukumar shirya wasannin kwallon kafa ta duniya FIFA, ta kaddamar da zagaye na 3, na kwas din koyar da ‘yan kwallo, dabarun warware takaddamar shari’a da kan faru a fannin wasanni. An dai kaddamar da kwas din ne a ranar Laraba, kuma a cikin sa ‘yan kwallo za su koyi dabarun fuskantar shari’a mai nasaba da sana’ar su.

An bude damar shiga kwas din ne a ranar 12 ga watan Afirilun nan zuwa 16 ga watan Yuni, kuma FIFA ta dora bayanai kan kwas din a shafin ta na yanar gizo domin masu bukata.

FIFA ta bayyana cewa, tana da tsawon tarihi, da kwarewa game da batutuwan shari’ar wasanni, tun kafin ma a kaddamar da kotun hukunta harkokin wasanni ta CAS, kasancewar FIFA din ta jima tana fuskantar irin wadannan ayyuka. Don haka ne a wannan lokaci, take son ‘yan wasa su ma su fahimci wannan muhimmin fanni na sana’ar su. An tsara gudanar da kwas din ne tsakanin watannin Satumba zuwa Disambar shekarar nan ta 2023 a biranen Madrid, da Buenos Aires da Zurich.


Lewandowski na fatan komawar Messi Barcelona

Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafar Barcelona Robert Lewandowski, ya ce yana da burin ganin Lionel Messi ya koma kungiyar ta su a kakar wasa mai zuwa.

Wasu kafofin watsa labarai na Sifaniya, sun bayyana cewa, Barcelona na ta kokarin ganin tsohon dan wasan na ta ya koma taka mata wasa a lokacin zafi na bana, kuma akwai alamun cewa, shi ma Lionel Messi dan asalin kasar Argentina, wanda a yanzu ke bugawa Paris Saint-Germain wasa tun daga shekarar 2021, yana da burin komawa Camp Nou.

Da yake tsokaci yayin zantawa da wata kafar watsa labarai ta Poland game da batun, Lewandowski ya ce “Ina fatan taka leda tare da Messi a Barcelona a kakar wasa mai zuwa. Idan har ya dawo, hakan zai burge kowa. Barcelona gidan sa ce. Bani da tabbacin abun da zai faru, amma ina fatan kakar wasa mai zuwa za mu buga kwallo tare".

A kakar wasa ta bana, Barcelona na hanyar lashe kofin La Liga, kasancewar kungiyar ta riga ta hada maki 13 cikin wasanni 28 da ta buga, inda ta dara abokiyar hamayyar ta Real Madrid.

A ‘yan shekarun baya bayan nan, Barcelona ba ta samu zarafin daukar kofin La Liga ba, sai dai a bana tana da kyakkyawar damar yin hakan, kuma idan ta samu wannan nasara, hakan zai yi matukar karfafa gwiwar ‘yan wasan ta.

A halin da ake ciki, Lewandowski ne dan wasa mafi yawan kwallaye a raga, a gasar ta La Liga, inda tuni ya jefa kwallaye 17 a raga.

Lewandowski mai shekaru 34, ya yi korafi game da yadda gasar cin kofin duniya ta hukumar FIFA ta shiga tsakiyar kakar wasanni ta bana, wanda hakan ya haifar da matsin lamba ga kulaflika, a gabar da mutane da dama ke fatan ganin ‘yan wasan gaba sun ci kwallaye da yawa a wasannin da ake bugawa. Sai dai ya ce duk da hakan, ‘yan wasa irin sa na yin iya kokarin ganin sun farantawa ‘yan kallo rai. Ya ce “Na gamsu cewa, za mu iya kara inganta kwazon mu na kai hare-hare ragar abokan fafatawa".