logo

HAUSA

Kasashen yamma na shafawa Sin bakin fenti bisa fakewa da karuwar jama’ar Indiya

2023-04-20 13:47:21 CMG Hausa

Asusun kula da yawan mutane na MDD wato UNFPA a takaice, ya fitar da rahoto kan “yanayin jimlar mutanen kasa da kasa a shekarar 2023”, inda ya yi hasashen cewa, adadin al’ummar kasar Indiya zai zarce na kasar Sin a tsakiyar bana, inda hakan zai sa Indiya ta kasance kasa mafi yawan mutane a duniya. Duk da cewa, lamarin sakamako ne na ci gaban yawan mutane kadai, wasu kafofin watsa labarai na kasashen yamma sun gabatar da rahotanni kamar na “Kasa mai saurin ci gaba za ta sauya”, ko “Tsarin kasa da kasa zai yi manyan sauye-sauye”, ko kuma “Dalilin yawan mutane zai hana farfadowar al’ummar kasar Sin”.

Hakika bai kamata a yi hasashen ci gaban kasar Sin bisa jimlar mutanenta kadai ba, ya dace a mai da hankali kan ingancin karuwar tattalin arzikin kasar. An lura cewa, karuwar tattalin arzikin kasar Sin a rubu’in farkon bana ta kai kaso 4.5 bisa dari, lamarin da ya shaida cewa, kasar tana samun ci gaba yadda ya kamata.

Kana ingancin al’ummar kasa shi ne mafi muhimmanci. A halin yanzu, adadin al’ummar Sinawa dake aiki ya kai kusan miliyan 900, kuma adadin yana karuwa da miliyan 15 a ko wace shekara. Ban da haka adadin Sinawa wadanda suka kai matakin digiri na farko a jami’o’i ya kai sama da miliyan 240, ko shakka babu kasar Sin tana cike da kuzari yayin da take kokarin raya tattalin arzikinta. (Jamila)