logo

HAUSA

Hare-haren bindiga dake hallaka Amurkawa na shaida gazawar gwamnati wajen kare hakkin bil Adam

2023-04-19 15:57:47 CMG HAUSA

DAGA MINA

Abokai, a karshen makon da ya gabata, fararen hular kasar Amurka sun sha fama da harbe-harben bindiga, wanda hakan ya haifar da asarar rayuka da dama. Bisa labarin da aka bayar, a daren ranar 15 ga watan nan, an samu aukuwar harin bindiga a garin Dadeville na gabashin jihar Alabama, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 4, baya ga sauran wasu 28 da suka ji rauni. Baya ga haka, a wannan rana, an fuskanci hare-haren bindiga a wata jami’a dake kudu maso gabashin jihar Pennsylvania, da wani lambun shan iska dake birnin Louisville na jihar Kentucky, hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane 2 da jikkatar wasu 4.

Bisa kididdigar da shafin intanet na Gun Violence Archive ya bayar, tun farkon wannan shekara zuwa yanzu, an samu aukuwar hare-haren bindiga a wuraren da jama’a ke taruwa har sau 163, lamarin da ya haifar da rasuwar mutane fiye da dubu 12.

A hannu guda kuma, kungiyar masu rajin kare mallakar bindiga ta Amurka ta NRA, ta gudanar da taron shekara-shekara a ran 14 ga watan nan, a birnin Indianapolis na jihar Indiana, bikin da masu goyon bayan mallakar bindiga da dama suka halarta, ciki har da wasu manyan jami’an jam’iyyar Republican wadanda suka bayyana goyon bayansu ga NRA.

A daya bangaren kuma, cibiyar dake rajin kare dokar hana hare-haren bindiga ta Giffords dake kasar Amurka, ta fitar da rahoto dake cewa, NRA mai mambobi fiye da miliyan 5 da kudade masu dimbin yawa, na da babbar alaka da harkokin siyasa da suka shafi zabuka a kasar, kuma hakan ya sa ‘yan siyasa ke dora muhimmanci sosai a kan kungiyar.

Cibiyar ta kara da cewa, yayin da ‘yan siyasar Amurka ke ja-in-ja da juna kan batun mallakar bingida, fararen hula ne kawai suke daukar asara. Gwamnatin Amurka wadda ake jinjinawa da sunan “Mai kare hakkin Bil Adama”, mutuncinta ya zube, sakamakon yawan aukuwar hare-haren bindiga dake addabar al’ummar kasar. (Mai zane da rubuta: MINA)