logo

HAUSA

Rawar da Sin ta taka wajen neman shimfida zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya

2023-04-19 09:56:55 CMG Hausa

A kwanakin baya ne, kasashen Saudiya da Iran suka sanar da maido da huldar diflomasiya a tsakaninsu bisa taimakon shiga tsakani na kasar Sin, tare da sake bude ofisoshin jakadancin juna, da ci gaba da gudanar da ragowar mu’amala kamar yadda aka saba a baya.

Ana sa ran wannan nasara da aka samu, za ta taimaka matuka ga shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali da kara hada kawuna a yankin gabas ta tsakiya.

Mataimakin zaunnanen wakilin kasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya, Geng Shuang ya bayyana a taron da kwamitin tsaron majalisar ya shirya game da batun kasar Yemen cewa, nasarorin da aka samu a wajen shawarwarin da tawagogin kasashen Saudiyya da Iran suka gudanar a Beijing, fadar mulkin kasar Sin za su kirkiro yanayi mai kyau ga daidaita halin da ake ciki a Yemen.

Kasar Sin tana son hada kai tare da sauran kasashe, don ci gaba da daidaita matsalar Yemen, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya baki daya. Wannan ya kara tabbatar da manfofin diflomasiyar kasar Sin ta neman tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun wadata a duniya. Matakin da masharhanta ke cewa, zai sanya kasashen duniya kara aminta da kasar Sin a matsayin mai kaunar zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)