logo

HAUSA

Bikin fesa ruwa na al'ummar kabilar Dai

2023-04-18 11:12:19 CMG Hausa

Ga yadda ake gudanar da bikin fesa ruwa a yankin Xishuang Banna mai cin gashin kansa na kabilar Dai da ke lardin Yunnan na kudu maso yammacin kasar Sin. Bikin gargajiya ne na al’ummar kabilar Dai wanda ke alamanta shiga wata sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyarsu, inda su kan fesa ruwa ga juna don nuna fatan alheri da farin ciki.(Lubabatu)