logo

HAUSA

Babbar kasa ita ce mai jagorantar sauran kasashe wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya

2023-04-18 17:20:23 CMG Hausa

A baya-bayan nan ana ta samu karuwar rikici tsakanin bangarorin Isra’ila da Falasdinu, lamarin da ke haifar da asarar rayuka da jikkata da tsaiko ga harkokin ibada. Rikici tsakanin bangarorin biyu abu ne da yaki ci yaki cinyewa, wanda ke haifar da damuwa a yankin gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya.

A matsayinta na kasa mai burin ganin dunkulewar duniya cikin zaman lafiya da ci gaba, kasar Sin ta bakin firaministanta Qin Gang, ta ce za ta samar da yanayin da ya dace na ganin an samu sulhu tsakanin bangarorin biyu.

Tabbas, lokaci ya yi da ya kamata a ce an samu mai shiga tsakani mai adalci, domin lalubo mafita da kawo karshen wannan daddaden rikici.

Da yake tattaunwa jiya Litinin ta wayar tarho da takwarorinsa na Falasdinu Riad Maliki da na Isra’ila Eli Cohen, Qin Gang ya ce a shirye kasarsa take ta tallafawa tattaunawar wanzar da zaman lafiya tsakanin bangarorin tare da samar da damar cimma nasarar hakan.

Hakika burin Sin shi ne ganin an samar da zaman lafiya da hadin gwiwa da hakuri da girmama juna tsakanin kasa da kasa da al’ummunsu. Dole a samu bambance bambance tsakanin bangarori daban daban, amma kai zuciya nesa da hakuri da wadannan bambance-bambance, shi zai kai ga samun tabbatuwar zama lafiya a duniya da ma samun ci gaba.

Kasar Sin misali ce, domin ta kasance kasa mai kabilu da mabiya addinai daban-daban, amma abun ban sha’awa shi ne, yadda wadannan al’ummomi suka amince da yanayinsu kuma suke hakuri da juna, sannan suke morar zaman lafiya mai inganci. Kasancewar na fito daga kasa mai mabanbantan kabilu da addinai, na kan yi matukar sha’awar yadda al’ummomin Sin ke zaune lafiya da juna ba tare da tsangwama ba. Don haka a ganina, babu kasar da ta fi dacewa wajen jagorantar sulhu tsakanin Falasdinu da Isra’ila, kamar kasar Sin.

Kamar yadda Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen dawo da dangantakar da ta yi tsami tsakanin Saudiyya da Iran, ina da yakinin za ta cimma nasara wajen shawo kan rikicin wadannan bangarori dake zaman makwabtan juna. Kuma a matsayin wadda ta tabbatar da zaman lafiya a cikin gida, na yi imanin idan har aka bata dama, Sin za ta iya gabatar da dabaru da matakai na shawo kan wannan rikici da yaki ci yaki cinyewa.

Lokaci ya yi da ya kamata sauran kasashen duniya su goyawa Sin baya kan wannan buri nata, a maimaikon bangaranci da rura wutar rikicin.

Matsayin babbar kasar da ta san ya kamata, shi ne jagorantar sauran kasashe wajen samar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa, kuma wannan, shi ne matsayin kasar Sin a duniya. (Faeza Mustapha)