logo

HAUSA

Me Ya Sa Karuwar Tattalin Arzikin Sin Na Watanni Uku Na Farkon Bana Ta Zarce Zaton Jama’a?

2023-04-18 21:38:42 CMG Hausa

A ranar 18 ga wata, kasar Sin ta bayar da alkaluman kididdigar tattalin arzikin kasar na watanni uku na farkon shekarar da muke ciki, inda aka nuna cewa, adadin GDP na kasar a rubu’in farkon bana ya kai kudin Sin yuan biliyan 28499.7, adadin da ya karu da kaso 4.5 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara. Lamarin da ya jawo hankalin kafofin watsa labarai na kasa da kasa, inda suka ba da labaran cewa, karuwar tattalin arzikin kasar Sin a watanni uku na farkon shekarar bana ta zarce zaton jama’a, kasar Sin na samun farfadowa cikin sauri, kasar Sin ta samu ci gaban tattalin arziki a farkon shekarar da muke ciki.

Hakika dai, ana samun rashin tabbaci wajen tafiyar da harkokin tattalin arziki a duk fadin duniya. Bisa wannan yanayin da ake ciki, an sha wuya wajen samun irin wannan sakamako mai kyau. Ba za a iya raba sakamakon da iyakar kokarin dukkanin al’ummar Sinawa wajen raya tattalin arziki ba.

Ana saran kasar Sin za ta kara samun ci gaban tattalin arziki sakamakon kyawawan manufofin da gwamnatin kasar take dauka. Har ma wasu manyan kamfanonin ketare suna ganin cewa, zuba jari a kasar Sin wajen raya ayyukansu zai ba su damar samun makoma mai haske.(Kande Gao)