logo

HAUSA

Zakeyeldinn Eltyeb: Kasar Sin gida na biyu ne nawa

2023-04-18 23:14:23 CMG Hausa

Zakeyeldinn Eltyeb Abobaker Khalid, dalibin kasar Sudan ne wanda a yanzu haka yake karatun digiri na uku a jami’ar koyon ilimin aikin gona ta Hebei dake birnin Baoding na kasar Sin.

A hirar sa da Murtala Zhang, malam Zakeyeldinn, wanda ya zo kasar Sin tun a shekara ta 2008, ya siffanta kasar a matsayin gidan sa na biyu, baya ga Sudan. Haka kuma a cewar sa, yana jin dadin mu’amala da mutanen kasar Sin sosai, har ma ci gaban kasar ya burge shi kwarai da gaske.

Malam Zakeyeldinn ya kuma bayyana ra’ayin sa kan muhimmancin hadin-gwiwar kasar Sin da kasar sa wato Sudan, har ma da Afirka baki daya, musamman a fannin aikin gona.

A karshe, malam Zakeyeldinn ya bayyana kyakkyawan fatan sa ga mutanen Sudan, wadanda suke son zuwa kasar Sin don karatu ko ziyara. (Murtala Zhang)