logo

HAUSA

Hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin ta dace da yanayin kasar

2023-04-17 11:05:49 CRI

A cikin shirinmu na yau, zan nuna muku yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi rangadi a birnin Guangzhou dake kudancin kasar. 

 

A ranar Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya kai ziyarar gani da ido a birnin Guangzhou, hedkwatar lardin Guangdong dake kudancin kasar, inda ya ziyarci wasu kamfanonin da suka hada da kamfanin LG Display mai hada na’urar kwamfuta, da kamfanin GAC AION mai samar da motoci masu yin amfani da wutar lantarki. Inda ya gane ma idonsa yadda ake aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen ketare cikin wani yanayi mai inganci, da raya sabbin fasahohi a bangaren masana’antu.

Shugaban ya yi nuni da cewa, akwai bambanci matuka tsakanin hanyar da kasar Sin take bi wajen zamanantar da kanta da na kasashen yamma. Ya ce, ba za a bi hanyar rarraba kawuna da wargaza wasu kasashe da kasashen yamma suka bi wajen zamanantarwa ba. Hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin, ta dogara ne kan hakikanin yanayin da kasar Sin ke ciki, ta kuma dace da yanayin kasar, tana da manufa, da tsare-tsare da dabaru, kuma za a ci gaba da aiwatarwa bisa mataki-mataki.