logo

HAUSA

Muhimmancin turaren wuta a cikin rayuwar mata a Nijar

2023-04-17 20:21:10 CMG Hausa

 

a wasu kabilun Nijar, kamar Barebari, da Larabawa, da Abzinawa har ma zuwa Hausa na taka muhimmiyar rawa wajen gyaran jikin diya mata da kawo shakar hayaki ko iska mai kanshi a cikin daki, dalilin haka ne turaren wuta yake shiga cikin harkokin tsaftar jiki da muhalli. Shin mene ne turaren wuta, kuma yaya ake hada shi, kuma mene ne amfaninsa a cikin rayuwar mata da gudunmuwar da yake kawowa mata.

Akwai wuya a yi maganar yankin Diffa, ba a yi maganar turaren wuta ba, ganin kasancewarsa wani muhimmin abu da ke gyara jikin diya mace, yaya ake hada wannan turaren wuta, kuma yaya ake kasuwancinsa.

Dalilin haka ne wakilin CMG dake Nijar Mamane Ada ya yi hira da Deluwa Abdu Dan Daura wadda ke sana’ar turaren wuta ga abin da take cewa:

Ko amarya aka yi yanzu turaren wuta shi ne kayan jerenta a daki, kuma turaren wutar nan yana da aminci tun da yana gyara mata da kyau, turaren wutar kala kala ne, kowane da hadin shi, akwai hadin da za yi sai mutum ya yi santi, Al-ut, gagam, sandal bangi, sandal rose, suntal, abba malam biyelanja, icce ne kala kala da za a hada kawai, to kayan hadinshi akwai garin sinta, akwai musur, akwai jawur, akwai kuma turare kala kala.

To ko minene amfanin turaren wuta ga jikin dan adam?

Turare wannan idan ka yi wanka, ka turara shi yana shiga jikinka ne sarai, idan ya shi jikinka, kamshin jikinka, ko zufa ka shiga ka yi, kamshin jikinka za ya fito ba ka wari, shi ya sa muke bukatar shi.

Ko ana iyar cewa wannan sana’a tana taimakawa zaman rayuwarku ta mata?

A harkar turare wannan fa, mun mai da shi sana’a babba ma, ba ta wasa ba, yanzu ni kam shi ne muke ci, muke sha, muke sutura, muke kome ni da iyalina da shi, mazajenmu sun bar mu muna sana’arshi, muna zuwa muna nemo wa muna kawowa kan gaskiya, muna murna bisa gare shi, muna jin dadi sarai, mata suna son shi kuma maza idan suka shiga daki suna jin dadin shi sosai.

Wace shawara ce za ku yi masu ciwon huka da ke son sanya turaren wuta cikin dakuna?

Turaren nan in dai ka san ana da ciwon huka ko asma nan, kana iya sanya shi tun da wuri ka dage dakin, idan ka dage shi ke nan, wannan hayaki ya fita, to kamshin yana nan lake a dakin.

Gaskiya, sana’ar turaren wuta na taimakawa mata sosai wajen samun abin dogaro da kai. Hakika dai, wasu hukumomin Nijar na kokarin kawo karshen matsalar samun wutar lantarki don inganta zaman rayuwar al’ummarta.

Lokacin zafi a Nijar, na tafiya tare da daukewar wutar lantarki, ko samun wutar lantarki lokaci zuwa lokaci. Domin fuskantar wannan matsala ce, gwamnatin Nijar ta kaddamar da gina tashar samar da wutar lantarki ta Gouro Banda a cikin watan Disamban shekarar 2022 a karkarar birnin Yamai, mai karfin megawatt 30. Wani matakin kawo karshen katse wutar lantarki ga mazauna biranen kasar.

Ita dai tashar samar da wutar lantarki ta Gorou Banda da ayyukanta suka kammala, zama wani abin hamdala da yin bankwana da matsalar daukewar wutar lantarki a kai a kai. A cewar ministan makamashi, Ibrahim Yacouba, burin gwamnatin Nijar shi ne na ganin Nijar ta rage dogaro da ketare ta fuskar makamashi, ta yadda za a samu babban tasiri kan layin wutar lantarki na yankin kogin Issa, inda yankunan Tillabery, Niamey da Dosso da za su samun wutar lantarki daga Gorou Banda.

A cewar Bruno Marty, darektan shirin alluna masu aiki da hasken rana dubu 55 da zai samar da Watt 540 tuni an kafa su, kuma haka zai zama wani kari bisa ga tashar Gorou Banda da ke samar da megawatt 75, tare da kuma tashar samar da wutar lantarki daga ruwa ta Goudel, mai samar da megawatt 89 idan kuma aka hada da megawatt 75 da Nijar ke saye daga Najeriya. Haka zai taimaka wajen bunkasa cigaban wutar lantarki a Nijar.

Saidai, a cewar Daoure Aboubacar, kwararre a kamfanin wutar lantarki na kasa NIGELEC, tare da magawatt 30 na Gorou Banda, Nijar da ke shigo da megawatt 75 daga Nijeriya, za ta ganin raguwar dogaronta da ketare. Idan kuma aka duba, gina madatsar ruwa ta Kandadji, mai karfin megawatt 130, shiri ne mai kyau da zai tabbata, da zai taimaka wajen kawo karshe matsalar wutar lantarki.

Mata na lura da fatansu sosai, yanzu zan yi muku bayani kan amfanin kankana na gyaran fata.

Kankana na daya daga cikin ‘ya’yan itace da ke da matukar tasiri a gyaran fata da kuma kawar da cututtukan fata masu dama. Tana dauke da sinadaran da ke gusar da maikon da ke fita a hanyoyin fitar gumi, wanda idan ya yawaita zai iya haifar da fesowar kananan kuraje.

Kankana na taka muhimmiyar rawa wajen gyaran fatar da take yawan yankwanewa, idan aka markade ta ba tare da an zuba mata ruwa ko kadan ba, kuma za a hade ne har ‘ya’yanta, aka zuba mata zuma kadan, ana shafawa a inda matsalar ta ke sau biyu zuwa uku a rana.

Kuma za a iya markade kankana tare da ganyen na’ana’a ana shafawa a fuska tsayin mintuna 30 kafin a wanke da ruwan dumi don magance matsalar kodewar fata, walau ta sanadiyyar zafin rana ko mutuwar kuraje da sauransu.

Sai dai wannan hadin ba shi da tasiri ga fatar da ta kode sanadin rashin abin da zai inganta ta na daga bangaren abinci ko ciyar da ita abin da ba ta bukata na daga mayuka da kayan kwalliyar da ake amfani da su.

A bangaren rage bayyanar shekaru a fata, kankana na taimako kwarai idan aka tanadi man zaitun, nono kindirmo, kwai. Za a hade su tare da kankana ana shafawa duk dare a kwana da shi.

Ko kuma a samu ayaba a hada ta da kankanar da aka markade sai a tarfa zuwa kadan a kwaba ana shafa wa fata.

Idan kuma gautsin fata ne matsalar ki ‘yar uwa, za ki iya amfani da kankana don samun laushi a fatarki. Ta yaya? Ki markaɗe kankana, sannan ki hada ta da man ridi, man kwakwa, sai man zaitun. Ana shafa wannan hadin da dare, tsayin minti talatin kafin a yanke. (Kande Gao)