logo

HAUSA

Yadda Tsoffin Abokai Ke Kafa Sabuwar Makoma A Tsakaninsu

2023-04-16 16:41:46 CMG Hausa

"Shugabannin kasashen Sin da Brazil sun kafa tarihi.", "Ziyarar da shugaban kasar Brazil Lula ya kawo kasar Sin, ta bude kofa ga kasar ta Brazil." kuma "Bayan ganawarsa da shugaban kasar Sin Xi Jinping, jakar shugaba Lula ta cike da yarjejeniyoyi da ma tsare-tsaren hadin gwiwa daban-daban." Ziyarar shugaban kasar Brazil Luiz Inácio Lula da Silva a kasar Sin wanda ya kammala jiya Asabar 15 ga watan Afrilu, ta samu jawabai masu kyau daga kafofin yada labarai na kasar Brazil da sauran sassan kasar. An kuma yi imanin cewa, shugabannin kasashen biyu sun tsara hanyar da za a bi a mataki na gaba na hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, tare da samar da sabuwar kyakkyawar makoma ga hadin gwiwar kasashen biyu.

A bana ne ake cika shekaru 30 da kulla huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen Sin da Brazil, kuma shekara mai zuwa za a cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya, kuma a wannan muhimmin lokaci, ziyarar da shugaba Lula ya kawo kasar Sin daga ran 12 zuwa 15 ga watan Afrilu, ta jawo hankalin jama'a matuka.

Bisa sakamakon shawarwarin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kuma sanarwar hadin gwiwa da bangarorin biyu suka fitar, ziyarar Lula a kasar Sin ta samu cikakkiyar nasara. Shugaba Lula na kasar Brazil ya bayyana cewa, babban burin 'yan majalisar dokokin kasarsa da dukkan bangarorin al'umma shi ne karfafa dangantakar da ke tsakanin kasar Brazil da kasar Sin a dukkan matakai.

Zaman lafiya da ci gaba da kuma zamanantar da kasar, su ne manyan burikan al’ummomin kasashen biyu wato Sin da Brazil. An yi imanin cewa, bisa jagorancin shugabannin kasashen biyu, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da Brazil a sabon zamani, za ta bunkasa zuwa sabon matsayi, wanda zai kawo karin alheri ga jama’ar kasashen biyu da sa kaimi ga hadin gwiwa tsakanin Sin da yankin Latin Amurka da ma zaman lafiya da ci gaban duk duniya.(Ibrahim)