Me ya sa 'yan kasuwar kasashen waje ke da kwarin gwiwa game da kasar Sin? Baje kolin kayayyakin masarufi ya ba da amsa…
2023-04-15 16:25:59 CMG Hausa
"Ina son kasar Sin, akwai babbar damar samun ci gaba a kasar." Guido.M.Ognibeni, shugaban wani kamfanin sarrafa kayan kwalliya na kasar Italiya ne ya bayyana haka, a gun bikin baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa karo na 3 da aka gudanar daga ranar 10 zuwa 15 ga wata a birnin Haikou na kasar Sin. Akwai 'yan kasuwan kasashen waje da dama da ke da kwarin gwiwa game da kasar Sin kamar wannan jami’in. Wannan bikin baje kolin kayayyakin masarufi shi ne karo na farko da kasar Sin ta gudanar da babban baje kolin kasa da kasa, tun bayan da aka yi nasarar gudanar da aikin rigakafi da shawo kan cutar COVID-19 yadda ya kamata, wanda ya jawo kayayyakin masarufi sama da 4,000 daga kasashe da yankuna sama da 60 na duniya.
Ga kamfanoni da yawa na kasashen waje, wannan bikin baje kolin ba kawai dandali ne na nuna samfurori ba, amma wata dama ce da za ta haifar a nan gaba. Tun bayan irin baje koli na farko da aka gudanar a shekarar 2021, kamfanonin kayan masarufi na kasa da kasa da dama, sun zauna a lardin Hainan, inda suka shiga cikin ayyukan raya cibiyar yawon bude ido da kayan masarufi ta kasa da kasa ta Hainan. A ganin wadannan kamfanoni, yanayin kasuwanci mai inganci da yadda Sin take bude kofofinta ga ketare, da matakai daban-daban na bude kofa da yarjejeniyar RCEP ta gabatar, musamman ma halin musamman na bude kofa da yankin ciniki cikin 'yanci ta Hainan ke ciki, dukkansu sun ba su damammakin samun ci gaba a kasar ta Sin, har ma da bunkasa a duk duniya.
A yau Asabar 15 ga wata ne, aka rufe bikin baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa karo na uku, sannan aka bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da fitarwa daga kasar Sin karo na 133. Bukukuwan baje kolin kasa da kasa da kasar Sin ke gudanarwa daya bayan daya, sun nuna yadda kasar ke ci gaba da cika alkawarin da ta dauka, wato kokarin mai da kasuwar kasar zama kasuwar duniya, kasuwar hada-hadar kudi, kasuwar kowa da kowa. Duk da yanayin da duniya ke ciki na rashin tabbas, tabbacin da kasar Sin ta samu ya kasance ginshikin kiyaye zaman lafiya da ci gaban duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)