logo

HAUSA

Amurka za ta iya daidaita batun bazuwar bayanan sirri kuwa?

2023-04-13 10:50:12 CMG Hausa

Tun farkon watan Maris na bana, ko ma kafin wannan lokaci ne, aka fara ganin wasu takardun sirri masu alaka da aikin soja na kasar Amurka, a shafukan sada zumunta da dama. Wadannan takardun sun kai fiye da 100, kana bayanan dake cikinsu, sun shafi yadda gwamnatin kasar Amurka ke da hannu a cikin yakin da ake yi tsakanin kasar Rasha da Ukraine, da yadda kasar ke sanya ido kan Ukraine, da Koriya ta Kudu, da dai sauransu.

A ranar Talata 11 ga wata, Lloyd Austin, sakataren tsaron kasar Amurka, ya gabatar da bayani dangane da batun bazuwar bayanan sirri a karon farko. A sa’i daya kuma, gwamnatin kasar ta sanar da alkawarinta na gano tare da cafke duk wanda ke da hannu wajen kwarmata takardun a shafukan sada zumunta. Hakan tamkar yarda ne da gaskiyar batun bullar bayanan sirri a fakaice.

Hakika yadda kasar Amurka ta rika sanya ido kan kawayenta cikin shekaru fiye da 10 da suka wuce, ba sirri ba ne. Kasar na yin haka ne don neman shawo kan kasashe kawayenta, ta yadda za ta iya yin babakere a duniya. A ganin kasar Amurka, moriyar kai ta fi zumunci. (Bello Wang)