logo

HAUSA

Wariyar launin fata da amfani da makamai barkatai ne ke rura wutar harbe-harben kan mai tsautsayi a Amurka

2023-04-13 16:48:01 CMG Hausa

A baya bayan nan masharhanta da dama na ta tsokaci game da yawaitar hare-haren bindiga, na kan mai tsautsayi da ake samu a Amurka, lamarin da akasarin masu fashin baki ke alakantawa da mummunar akidar nan ta wariyar launin fata mai tsohon tarihi a kasar, da son cin zali na turawa masu rajin fifita fararen fata, tare da yawaitar mallaka, da amfani da makamai tsakanin fararen hular kasar.

Alkaluma sun nuna cewa, daga farkon shekarar nan ta 2023 zuwa yanzu kadai, an samu harbe-harben kan-mai-uwa da wabi har 146, ciki har da wanda aka hallaka wasu ’yan makarantar firamare 3, da wasu manya 3 a birnin Nashville, da wanda ya auku a jihar Kentucky a ranar Litinin, wanda ya sabbaba rasuwar mutane 4.

A fili take cewa, Amurkawa da shekarun haihuwarsu ya kai 18, na da ikon saye ko rike bindiga, ciki kuwa har da manyan bindigogi masu hadarin gaske, wanda hakan ke kara ta’azzara yanayin tsaron fararen hula. Sannu a hankali, tashe-tashen hankula masu nasaba da harbin bindiga sun samu gindin zama a Amurka. Masana da yawa na cewa, baya ga batun saukin mallakar bindigogi, akwai kuma matsalar fatara, da gallazawa da wasu sassan al’ummun kasar ke fuskanta, wadanda su ma ke kara rura wutar wannan matsala.

Kisan bakar fatan nan mai suna George Floyd, da wasu ’yan sanda fararen fata suka yi a birnin Minneapolis a shekarar 2020, shaida ce da ta kara fayyace yadda wasu sassan al’ummar Amurka ke fuskantar nuna wariya da kyama. Alkaluma sun tabbatar da cewa, mutane da ba asalin fafaren fata ba ne, sun fi fuskantar muzgunawa a Amurka. Kuma wani karin abun takaici ma shi ne yadda wasu ’yan siyasar kasar ke amfani da kalamai na tunzura akidar nuna wariya, a matsayin dabar siyasa ta jan ra’ayin magoya baya.

A daya hannun kuma, mun san cewa cinikin makamai wani ginshiki ne na bunkasar tattalin arzikin Amurka, don haka mamallaka kamfanonin kera makamai, da masu nema musu goyon baya wajen ’yan siyasa, suka zamo kadangaren bakin tulu, wajen dakile matsalar raba fararen hular kasar da makamai masu hadari.

Abun tambaya a nan shi ne, idan aka gaza kare rayukan al’umma, shin ina sauran wani batun kare hakkin bil adama? 

Maimaituwar hare-haren bindiga kan fararen hula a sassan Amurka, na nuni ga yadda gwamnatin kasar ta kasa fahimtar cikakkiyar ma’anar ’yancin bil adama, wanda ya hada da kare rayukan yara kanana, da matasa daga farmakin ’yan bindiga dadi. (Saminu Alhassan)