logo

HAUSA

Me ya sa kasashe da yawa ke warware tasirin dalar Amurka?

2023-04-13 21:29:43 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

A cikin kwanakin baya, kasashe da dama na daukar matakai a kokarin warware tasirin dalar Amurka, ciki har da kasashen Latin Amurka, da na gabas ta tsakiya, sai kuma kasashen ASEAN, da Rasha da Iran, har ma da wasu kasashen Turai, bi da bi sassan suna ta bullo da shirye-shiryensu, ko kuma daukar matakai, don neman gudanar da ciniki da kudaden da ba dalar Amurka ba. A Afirka ma, gwamnatin Kenya ta sanar da yin watsi da dalar Amurkar wajen shigar da makamashi, inda har ta cimma yarjejeniya da kasar Saudiyya, kan sayen makamashi da kudinta na shilling. Ita kuwa ministar harkokin wajen kasar Afirka ta kudu Naledi Pandor cewa ta yi, kasashen kungiyar BRICS na nazarin kafa wani tsarin ciniki mai adalci bisa bankin NDB wanda aka kafa a shekarar 2014, ta yadda za a kai ga warware tasirin dalar Amurka.

Amma me ya sa kasashen ke wannan kokari? Lallai tun bayan da dalar Amurka ta kafa babakere a duniya bisa tsarin Bretton Woods da aka kafa a shekarar 1944, kasashen duniya sun sha wahalhalun da dalar ta haifar musu. Kasancewar dala muhimmin kudin da aka fi yin amfani da shi wajen gudanar da ciniki tsakanin kasa da kasa, Amurka  ta sha yin amfani da dala wajen kakaba takunkumi a kan wasu kasashen da suka ki biyayya gare ta, baya ga yadda ta rika cusa matsalolin tattalin arzikinta ga sauran kasashen duniya, tare da kwace arzikinsu ta hanyar daidaita kudin ruwa kan dala.

Idan ba a manta ba, bayan aukuwar rikici tsakanin Ukraine da Rasha, Amurkar ta hada kan kasashe da dama wajen kakaba wa Rashan takunkumi, matakin da ya haifar da mummunan tasiri ga cinikin fitar da hajojin kasar, kuma hakan ya nuna yadda take amfani da dalarta a matsayin makami na nuna fin karfi.

Sai kuma daga watan Maris na bara, asusun ajiyar kasar Amurka ya sha daga kudin ruwa har sau tara, a yunkurin daidaita matsalar hauhawar farashin kaya da take fuskanta a gida, matakin da ya haifar da hauhawar farashin kaya, da tabarbarewar tattalin arziki a kasashen duniya da dama. Kamar dai yadda yadda tsohon sakataren kudin kasar ta Amurka John Connally ya fada, “dala kudinmu ne, amma kuma matsala ce gare ku.”

A gabanin yadda kasashen duniya ke daukar matakai na warware tasirin dala, dan majalisar dattawa daga jihar Florida Marco Rubio, ya bayyana bakin cikin sa yana cewa, “Nan da shekaru biyar masu zuwa, babu zancen takunkumi, kasancewar karin kasashe na ciniki da kudin da ba dala ba, a gaba ba wani mataki da za mu iya dauka don sanya musu takunkumi.”

Abin haka yake, zamanin da Amurka ke amfani da dalarta wajen kafa babakere a duniya na dab da karewa, kuma ya kamata ‘yan siyasa irinsu Marco Rubio, su yi tunani sosai a kan me ya sa sassan kasa da kasa ke neman warware tasirin dala. In dai har Amurka ta ci gaba da nuna fin karfi da babakere, kuma ta gudanar da harkoki ba bisa ka’idojin duniya ba, tare da haifar da mumunnan tasirin ga tattalin arzikin duniya, to, tabbas za ta ga bayan matsayin dalarta. (Mai Zane:Mustapha Bulama)