logo

HAUSA

Wane irin kuzarin da ke addabar kasuwancin waje na kasar Sin?

2023-04-13 22:14:13 CMG Hausa

Bisa alkaluman da hukumar kwastan ta kasar Sin ta fitar a yau Alhamis 13 ga wata, an nuna cewa, hada-hadar cinikayyar waje ta Sin ta kai yuan tiriliyan 9.89 a rubu’in farko na shekarar 2023 da muke ciki, wato ta karu da kaso 4.8 bisa dari, idan an kwatanta da na shekarar bara.

Yanayin da ake ciki yanzu, na koma bayan bukatun hajojin Sin daga waje, wanda hauhawar farashin kayayyaki na duniya, da tafiyar hawainiya ta fuskar tattalin arziki da manyan kasashen duniya suka fuskanta, sun kawo wahalhalu masu tarin yawa ga kasar Sin a fannin bunkasuwar cinikayyar waje.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, cinikin waje na kasar Sin ya jure wa gwajin da aka yi, kuma ya aza harsashi mai kyau na tabbatar da samun ci gaban cinikayyar waje mai inganci yadda ya kamata a duk shekarar.

Cinikayyar waje ta kasance wani fanni na ma'aunin tattalin arzikin kasar Sin. Bankin duniya ya fitar da wani rahoto kan yanayin tattalin arziki a gabashin Asiya da yankin tekun Pasifik a karshen watan Maris, wanda ya kai adadin karuwar tattalin arzikin kasar Sin zuwa kashi 5.1% a shekarar 2023, wanda ya zarce na kashi 4.3% da aka yi hasashen a watan Janairu.

Yanayin kasa da kasa da ake ciki a yanzu yana da tsanani, kuma mai rikitarwa ne, kana har yanzu makomar cinikayya na fuskantar matsin lamba. Amma abin da ya fi muhimmanci a gane shi ne, bisa ci gaban ayyukan tattalin arzikin kasar Sin baki daya, ana sa ran cinikayyar waje ta kasar za ta ci gaba da inganta, da kuma kawo karin moriya ga duniya baki daya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)