logo

HAUSA

Hakika maganar “tarkon bashi” tarko ne na tunani

2023-04-12 18:39:34 CMG Hausa

Wani abokina ya kan buga mana waya daga jihar Kano ta Najeriya don mu gaisa da juna, sai dai yawan waya da ya buga mun a wadannan kwanaki ya ragu. Daga baya na fahimci dalilin da ya sa haka, wato hauhawar farashin kaya ta sa shi fuskantar matsin lamba a fannin rayuwa, don haka ya fara tsimin kudin da yake kashewa a fannin sadarwa. Misalinsa ya nuna yadda ake fama da mawuyacin hali a kasar Najeriya, gami da kasashe daban daban na Afrika.

Wannan yanayi mai wuya a fannin tattalin arziki ya sa kasashen Afrika samun matsalar biyan bashin da ake binsu. Ganin haka ya sa wasu jami’an kasar Amurka sake fara kokarin haifar da matsala ga huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, inda suka ce wai kasar Sin ta yi karan tsaye ga aikin yafewa kasashen Afrika basusukan da ake binsu. A bisa ra’ayin wasu mutane na kasar Amurka, da na wasu kasashen dake yammacin duniya, duk wani rancen da kasar Sin ta samar “tarkon bashi” ne, wanda ke da nufin lahanta moriyar kasashen Afrika.

Batun nan ya sa ni tunawa da wata tsohuwar maganar da mu Sinawa mu kan fada, wato “Idan ana neman dorawa wani laifi, to, ba za a rasa hujja ba.” Sai dai karya kome dadinta, ba gaskiya ba ce.

Mene ne gaskiyar lamarin?

Na farko, bashin da kasar Sin ta samar wani karamin bangare ne na daukacin basussukan da ake bin kasashen Afrika.

Wata kungiyar da ba ta gwamnati ba dake kasar Birtaniya mai suna Debt Justice ta sanar da wani rahoto a watan Yulin bara, wanda ya nuna cewa kashi 35% na basusukan da kasashen Afrika suke ci sun zo ne daga kamfanonin ba da rance masu zaman kansu dake kasashen yammacin duniya, inda adadin kudin rancen da suka samar wa kasashen Afrika ya ninka na kasar Sin har sau 3. Ban da wannan kuma, su manyan hukumomin hada-hadar kudi na kasa da kasa, irinsu bankin duniya, da hukumar ba da lamuni ta duniya, su ma sun samar da dimbin bashi ga kasashen Afrika, kana manyan ’yan kasuwa masu rike da mafi yawan hannayen jarin wadannan hukumomi suna kasar Amurka da kuma kasashen Turai.

Na biyu shi ne, kasar Sin na samar da bashi mai rangwamen kudin ruwa ga kasashen Afrika, gami da kokarin rage musu matsin lamba a fannin biyan bashi.

Bashin da kasar Sin ke samar wa kasashen Afrika, ruwansa ya yi kasa da ruwan bashin da sauran kasashe ke bayarwa wanda ya kan kai kashi 5%, kana Sin ba ta taba gindaya wani sharadi maras dacewa yayin da take ba da rance ba. Ban da haka, kasar Sin tana kokarin taka rawa a shawarar da kungiyar G20 ta bayar ta dakatar da biyan bashi, inda ta kulla yarjejeniya ko kuma cimma matsaya ta tsawaita wa’adin biyan bashi tare da kasashe 19 dake nahiyar Afrika. Cikin wani sabon rahoton nazari da jami’ar Johns Hopkins ta kasar Amurka ta gabatar, an ce yawan bashin da kasar Sin ta dakatar da lokacin biyansa ya kai kashi 63% cikin dukkan basusukan da mambobin kungiyar G20 suka tsawaita wa’adinsu.

Sa’an nan na 3 shi ne, ba kasar Sin ce ta sa kasashen Afrika fuskantar mawuyacin hali a fannin tattalin arziki, da kasa biyan bashin da ake binsu ba.

Yadda bankunan kasar Amurka suka kara yawan ruwan ajiyar kudi, da karuwar darajar dalar Amurka, suna janyo dimbin kudi zuwa kasuwannin kasar Amurka daga kasashe daban daban. Lamarin da ya sa kasashen Afrika karancin jarin da ake zuba musu, da rashin kudin musaya da ake bukata yayin da ake ciniki tsakanin kasa da kasa, kana kudin da suke kashewa wajen neman bashi a kasuwannin kasa da kasa ya karu sosai. Ban da haka, kasar Amurka na ta kokarin neman tsananta yanayin da ake ciki a yakin da ake yi tsakanin kasar Rasha da ta Ukraine, abun da ya haddasa daddadiyar hauhawar farashin abinci, da na sauran kayayyakin masarufi, ta yadda kasashen Afrika ke fuskantar matsin lamba sosai a fannin tattalin arziki. Wadannan dalilai da tasirin annobar cutar COVID-19, su ne suka jefa kasashen Afrika cikin wani mawuyacin hali.

Sai dai wasu mutane na kasar Amurka, da na wasu kasashen yammacin duniya, sun rufe ido a gabanin ainihin abun da ya faru, inda suka dinga ruta maganar “ tarkon bashi” na kasar Sin. Hakika suna neman sanya kasashen Afrika fadawa cikin tarko na tunani. Wannan “tarko” wata fasaha ce da mutanen kasashen yammacin duniya su kan yi amfani da ita a lokacin da suke muhawara da juna, wato “Poisoning the well” (zuba guba cikin rijiya). Idan an zuba guba cikin rijiya, ba za a iya shan ruwan da aka debo daga rijiyar ba. An yi amfani da kalmomin wajen siffanta yadda ake shafa wa wani mutum kashin kaza. Sa’an nan bayan da aka bata sunan mutum, to, ba za a sake amincewa da maganarsa ba. Abun da wasu mutane na kasar Amurka da na wasu kasashen yammacin duniya suke nema ke nan, wato bata sunan kasar Sin, don girgiza imanin da kasashen Afrika suke da shi kan kasar ta Sin, ta yadda za a lalata hulda mai kyau dake tsakanin kasashen Afrika da kasar Sin, da hana kasashe masu tasowa samun ci gaba. Kawai suna neman kare matsayin kasashen yamma na kan gaba a duniya, da ikonsu na ba da umarni ga saura, musamman ma a fannin kula da harkokin kasa da kasa.

Abokaina, a ganinku, za su cimma burinsu kuwa? (Bello Wang)