logo

HAUSA

CICPE: Sin za ta ci gaba da bunkasa samar da kayayyaki masu inganci

2023-04-12 08:07:16 CMG Hausa

A ranar Litinin 10 ga wata ne, aka bude bikin baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa na kasar Sin karo na 3 a birnin Haikou na lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin. Ana sa ran nuna kayayyakin masarufi masu inganci fiye da 4000 daga kasashe da yankuna guda 65 yayin bikin da za a gudanar har zuwa ranar 15 ga wata. 

Yawan kasashe mahalarta bikin da tambura da kuma kamfanoni masu sayayya da sauran ma’aunai sun karu a bana. Ban da wannan kuma, kamfanoni da hukumomin sana’o’i daban-daban na lardin Hainan sun bayyana aniyarsu ta shiga bikin, don amfani da wannan zarafi mai kyau wajen yin mu’amala da kamfanonin cikin gida da na waje, tare da kokarin samun moriya tare.

Ciniki ta intanet wata muhimmiyar sana’a ce da lardin na Hainan yake goyon baya. Yankin cinikin intanet tsakanin Sin da ketare ta Sanya, ya halarci bikin a karon farko, tare da gwada amfanin gona da fasaha fiye da nau’o’i 10.

An yi kiyasin cewa, yawan mutane mahalarta bikin zai zarce dubu 300, sassan kasuwanci za su gabatar da ayyukan samar da rangwame iri daban-daban ga masu sayayya a matsayin kiran kasuwa da ma habaka karfin sayayya.

Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kuma mataimakin firaministan majalisar gudanarwar kasar Sin He Lifeng, ya bayyana yayin bude bikin cewa, kasar Sin ta zama kasa ta biyu mafi girma a kasuwar kayayyakin masarufi a duniya. Baya ga kasancewarta babbar kasuwar kasa mai tasowa.

A shekarar 2022, jimillar darajar kayayyakin masarufi da aka sayar, ya kai yuan triliyan 44, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 6.4, karuwar kashi 7.9 bisa 100 a cikin shekaru goma da suka gabata.

Domin samun ci gaba, kasar Sin za ta mai da hankali kan kara samar da kayayyaki da ayyuka da hidimomi masu inganci, da tallafawa kamfanoni don karfafa bincike da ci gaba, da karfafa sabbin hanyoyin amfani da su, da inganta tsarin samar da kayayyakin masarufi. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)