Bunkasar wasannin hunturu ya samar da kyakkyawar makoma ga al’ummun Xinjiang
2023-04-13 16:12:44 CMG HAUSA
Yayin da wasannin motsa jiki da ake gudanarwa a lokacin hunturu ke kara samun tagomashi a sassan kasar Sin, al’ummun kasar da dama na bayyana kyakkyawan fata, game da moriya mai yawa da hakan zai haifar gare su a nan gaba.
Ga wata mata mai suna Biregul, wadda ke zaune a kauyen Hemu na tsaunin Altay dake jihar Xinjiang, a arewa maso yammacin kasar Sin, lokacin hunturu yana nufin lokaci na zama shiru a tsawon lokaci.
Amma a shekarar 2021, lokacin da aka bude wurin wasan zamiyar kankara na “ski” mai nisan kilomita 5 daga gidan ta, abubuwa sun fara sauyawa, kuma nan da nan hada-hada ta fara budewa a hanyar dake kusa da gidan ta.
Hanyar dake daura da gidan Biregul, ta ratsa yankin Altay, ta hada gundumomin Burqin da Hemu, wurin da dusar kankara kan kasance har sama da watanni 5, kuma tsayin ta daga kasa kan kai mitoci da dama. Yayin wasannin lokacin hunturu, ana ganin karin ababen hawa dauke da jakukkunan kayan wasan zamiyar kankara na wuce ta wurin a akai-akai.
Ana iya cewa, har yanzu karsashin wasannin kankara da na dusar kankara da gasar Olympics ta birnin Beijing ta shekarar 2022 ta bari bai gushe baki daya ba, domin kuwa har yanzu wasannin hunturun sun zamo wani bangare na rayuwar al’ummun yankin, lamarin da ya haifar da babban sauyi ga tattalin arziki, da zamantakewar al’ummar yankin.
Xinjiang, jiha ce mai yanayi mai kyau, kuma mai wurare dake iya ba da damar gudanar da wasannin zamiyar kankara na “ski”, kuma jiha ce da ta wuce gaba wajen juya akalar kasuwar wannan fanni na wasanni, inda jihar ta zamo daya daga wurare mafiya jawo hankalin masu yawon bude ido a lokacin hunturu. Bugu da kari, mazauna wannan yanki sun samu sababbin guraben ayyuka yi, da hada-hadar kasuwanci mai yawa, wanda hakan ke haifar musu da karin kyakkyawar rayuwa.
Shekaru ba sa hana wasa
Nie Rongchen mai shekaru 6 a duniya dake jihar Xinjiang, tuni ya fara more wasan zamiyar kankara, inda yake zamiya daga tudu mai nisa tare da nuna kwarewa. Yayin zubar dusar kankara, yana yin atisaye a wurare da dama na gandun wasan kankara dake Altay, da wanda ke Urumqi fadar mulkin jihar.
A halin yanzu, Xinjiang na da gandun wasan kankara guda 5 masu inganci wadanda ke yankunan tsaunukan Tianshan da Altay. Alkaluman kamfanin lura da bunkasar yawon bude ido na Xinjiang Altay, sun nuna cewa, gandun wasan zamiyar kankara na Jiangjunshan, da na Koktokay da na Jikepulin, wadanda ke karkashin kulawar kamfanin, sun karbi ‘yan wasan zamiyar kankara 10,178 a ranar 25 ga watan Janairu.
A gandun wasan hunturu na “Hanyar Siliki” kuwa, wato daya daga wuraren wasan kankara mafi girma dake Urumqi, Liu Zhihua ya shiga gungun masu nishadi, wadanda ke gudanar da zamiyar kankara kanana da tsofaffi, har da wadanda suka kai shekaru 88.
Liu ta fara wannan wasa ne tun daga shekarar 2007, lokacin tana da shekaru 72. Kuma har zuwa yanzu, kamar sauran Sinawa masu yawa, ta ci gaba da kwashe mafi yawan lokutan rayuwar ta tana kula da jikokin ta, da kallon talabijin, da wasan mahjong. Ga wannan dattijuwa, wasan zamiyar kankara hanya ce ta wanzar da kuruciyar ta. A baya bayan nan, wasu lokutan ta kan yi wasan zamiyar kankara har na tsawon sa’o’i 2, karkashin kulawar mai horaswar ta. A cewar Liu "Na gwammace na fadi a tudun zamiyar kankara da na kwanta a gadon jinya". Liu na cike da murmushi ta kara da cewa “ Buri na shi ne na ci gaba da wannan wasa da nake so har zuwa lokacin da ya zama dole na dakata”.
Albarkacin tsayin lokacin da kankara ke kasancewa a duk shekara, da ingancin kankarar, da wurare masu yanayi daban daban, a shekarun baya bayan nan, jihar Xinjiang na samun adadin jama’a mai tarin yawa dake zuwa domin wasanni, kana jihar na jan hankalin dubun dubatar masu sha’awar wasan zamiyar kankara.
A lokacin zubar kankara na bara, Peng Chao ya yi hayar wani gida na katako wanda ke Hemu, ya kuma mayar da shi wurin gudanar da ayyuka domin masu sana’o’in da suka shafi lura da kayan wasannin kankara, da horas da masu yin zamiyar kankara.
Bisa la’akari da bunkasar wasannin kankara da dusar kankara a kasar Sin, Peng ya yi imanin cewa, kasuwar fannin za ta ci gaba da fadada da kara inganta, kuma adadin masu wasan zamiyar kankara za su karu, kana za su kara gogewa, yayin da karin wasu daga cikin su za su nemi samun kwarewa sama da wadda suke da ita. Ya ce "Irin wadannan ‘yan wasa masaukin su shi ne Altay, mu kuma za mu jira zuwan su".
Sabon zabi sabuwar makoma
Mayirbek Chihsi, wanda ya fito daga zuri’ar makiyaya, yake kuma rayuwa a tsaunukan garin Koktokay dake kauyen Altay na gundumar Fuyun, ya zama dan wasan zamiyar kankara na farko a cikin dangin sa.
A shekarar 2018, matashin dan asalin kabilar Kazakh, ya bar rayuwar makiyaya, ya kuma fara aiki a wani gandun wasan kankara dake kusa da garin su. Ta hanyar kwarewa da ya samu tun lokacin kuruciya, lokacin da yake amfani da allon katako da ya lullube da wata fata mai gashi, a yanzu bayan shafe shekaru 2 yana samun horo, Mayirbek Chihsi ya zamo kwararren mai horas da masu wasan zamiyar kankara, da masu aikin ceton ‘yan wasan.
Tawagar masu ceton ‘yan wasa wadda Mayirbek Chihsi ke jagoranta, na kunshe da ma’aikata da ya horas su 22, kuma dukkanin su tsoffin makiyaya ne wadanda suke da kwarewa a fannin zamiyar kankara, sun kuma kware wajen shiga ko ina a gandun wasan na zamiyar kankara. A ‘yan shekarun baya bayan nan, mambobin tawagar sun ceto rayukan masu wasan zamiya da dama, wadanda suka makale cikin dusar kankara mai zurfi.
A bana, Koktokay na cikin wurare 19 da jihar ta zaba, a matsayin muhimman wuraren dake karkashin ikon ta, a fannin wasan zamiyar kankara ga daukacin ‘yan wasa na kasa baki daya.
Wani rahoron shekara wanda cibiyar bunkasa hada-hadar yawon shakatawa mai nasaba da wasannin kankara ta kasar Sin ta fitar, ya nuna cewa, tsakanin lokacin zubar kankara na shekarun 2024 zuwa 2025, fannin samun nishadi da bude ido na wasannin kankara a kasar Sin na kara fadada, inda ake hasashen zai janyo baki da yawan su ya kai sama da miliyan 520, adadin da zai samar da kudaden shiga har sama da kudin Sin biliyan 720, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 106, wanda hakan ya mayar da fannin babban jigo na bunkasa fannin yawon bude mai nasaba da lokacin hunturu, da bunkasar tattalin arziki mai nasaba da wasannin kankara.
Ta cin gajiya daga bunkasar wannan fanni, karin mazauna Xinjiang na da burin fadada hada-hadar kasuwancin su, ta yadda za su ci karin gajiya daga wasannin kankara.
Gandun “Hanyar Siliki”, wanda ke fadar mulkin jihar, shi kadai ya samar da guranen ayyukan yi da yawan su ya haura 500 ga manoma da makiyayan kauyuka sama da 20, baya ga masu horas da ‘yan wasan kankara sama da 300, da kuma ma’aikatan samar da abinci kimanin 114.
Biregul ‘yar asalin kauyen Hemu, wadda ke yin sana’ar bayar da hayar dakunan kwana ga masu ziyara a gidan ta na katako tun daga shekarar 2018 ta ce a shekarun baya, masu ziyara kalilan ne ke zuwa kauyen su a lokacin hunturu. Ta ce “Bisa lura da karancin masu zuwa, da kudin makamashin dumama dakuna, da kudin biyan ma’aikata, akwai lokacin da muka yi tunanin rufe sana’ar ta mu".
Sakamakon bude gandun wasan kankara na “Jikepulin” a lokacin zubar kankara da ya gabata, masu sha’awar wasan dake zuwa kama dakunan kwana sun karu matuka. Dakunan da Biregul ke bayarwa haya sun zama daya daga wuraren saukar baki da dama dake karuwa a wannan wuri. Yanzu haka akwai irin wadannan gidaje 113, wadanda ke kunshe da sama da gadajen kwana 3,000 a wannan kauye na Hemu a lokacin sanyi na bana, kamar dai yadda kwamitin jagorancin yankin Kanas ya bayyana.
Daga lokacin zubar kankara na shekarar 2016 zuwa 2017, da kuma shekarun 2021 zuwa 2022, adadin masu yawon bude ido dake zuwa Altay sun karu daga miliyan 1.94 zuwa miliyan 11.96, Kuma kudaden shiga da fannin ya samar sun karu daga yuan biliyan 1.17 zuwa biliyan 10.29, bisa kididigar hukumomin gundumar.
Biregul ta ce "Masu zuwa wasan zamiyar kankara na zama a nan har tsawon akalla kwanaki 3 zuwa 5, wasu kuma kan kai har makwanni 2. Kaza lika wasu kan yi hayar dakunan da za su zauna tun daga farkon shekara, har zuwa lokacin hutun bikin bazara na kasar Sin".