Sin: Fannin Sayayya Da Na Yawon Shakatawa Na Kara Farfadowa A Rubu’in Farko Na Bana
2023-04-10 07:46:38 CMG Hausa
Barka da watan Ramadan, masu kallonmu. Yayin da hada-hadar tattalin arziki ke kara komawa zuwa yanayi makamancin gabanin bullar anobar COVID-19 a nan kasar Sin, harkokin tafiye-tafiye, da yawon bude ido, da sayayya na kara farfadowa, a rubu’in farko na shekarar nan ta 2023.