logo

HAUSA

Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” ta sauya rayuwar jama’a a sassan duniya

2023-04-08 14:38:50 CMG Hausa

Shawarar ziri daya da hanya daya, shawara ce da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a shekarar 2013. Da farko shawarar ta mayar da hankali ne kan zuba jari a fannin ababan more rayuwa, da Ilimi, da gine-gine, da hanyoyin mota da layin dogo, da rukunin gidajen kwana, da tashoshin samar da wutar lantarki, da sauran muhimman fannoni da dan-Adam ke bukata.

Bayanai na nuna cewa, shawarar ta kasance tsarin da ya gudanar da ayyukan more rayuwa da zuba jari mafi girma a tarihi, inda ya shafi sama da kasashe 68, ciki har da kaso 65 cikin 100 na yawan al’ummar duniya, da kaso 40 cikin 100 na ci gaban GDPn duniya a shekarar 2017.

Shawarar Ziri daya da hanya daya, ta yi nasarar magance gibin ababen more rayuwa, kana tana da karfin bunkasar tattalin arzikia yankin Asiya da fasifik da yankunan tsakiya da gabashin turai. Masana sun yi imanin cewa, shawarar tana da muhimmanci sosai wajen bunkasa alakar kasa da kasa. 

Bugu da kari, shawarar, ta baiwa kasar Sin damar raba dabarun ci gaban ta da sauran kasashen Afirka masu tasowa, wanda hakan ya haifar da nasarar kammala layukan dogo, da titunan mota, da tashoshin jiragen ruwa da na sama, a birane da garuruwa a sassa daban-daban na kasashen Afirka da Asiya da sassan duniya, ayyukan da suke taka muhimmiyar rawa a fannin bunkasa ci gaban tattali da zamantakewar irin wadannan kasashe. Bayanai na nuna cewa, tun bayan da aka gabatar da shawarar, ya zuwa yanzu kasar Sin ta yi aiki tare da kasashen da abin ya shafa, wajen zurfafa hadin gwiwar moriyar juna bisa ka'idar yin shawarwari mai zurfi, da ba da gudummawar hadin gwiwa, da samun moriyar juna, kana ta cimma nasarori masu tarin yawa.  Babu shakka, shawarar “Ziri daya da hanya daya”, ta zama wani babban dandalin hadin gwiwa na kasa da kasa mafi girma a duniya. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)