logo

HAUSA

Me ya sa Macron ya yi imanin cewa Sin da Faransa na da babbar dama tare

2023-04-08 21:50:28 CMG Hausa

“Muna da abubuwa da dama da za mu iya yi cikin hadin gwiwa. Allah ya ja zamanin hadin gwiwar dake tsakanin Faransa da Sin. Zumuncin ba na yau ba ne! ” A ranar 7 ga Afrilu ne, shugaban Faransa Macron ya wallafa wani sharhi cikin harsunan Sinanci, da Turancin Ingilishi da Faransanci a dandalin sada zumunta, yana mai bayyana kawo karshen ziyararsa a kasar Sin. A wannan rana, jaridar Financial Times ta kasar Burtaniya, ta ruwaito manazarta na cewa, “A karshe, ziyarar ta Macron na da ma’ana mai kyau, ko dai ta karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kasuwanci da kasar Sin, ko kuma ta inganta batun warware rikicin kasar Ukraine.”

A halin yanzu, halin da ake ciki yanzu duniya na fuskantar rikice-rikice da karuwar rashin tabbas. Kasashen Sin da Faransa na fuskantar kalubale na bai daya da ba da kariya, da kuma ayyukan raya tattalin arziki da kiyaye rayuwar jama’a. Haka kuma suna da ra’ayi iri daya kan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya, kamar rikicin Ukraine da batun nukiliyar kasar Iran. Ci gaba da kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ba wai kawai za ta amfanar da kansu ba, har ma tana sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar Sin da Turai, da inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. (Ibrahim)