logo

HAUSA

Ana iya ganin cikakkiyar darajar tsarin demokuradiyya a kasar Sin

2023-04-07 18:36:17 CMG Hausa

Daga ranar 22 zuwa 23 ga watan Maris, an shirya wani taron tattaunawa da ya shafi tsarin demokuradiyya a birnin Beijing na kasar Sin, wanda ke da taken “Demokuradiyya: Fa’ida ta bai daya ga daukacin bil-Adama. Wannan biki da aka gudanar da shi a karo na biyu, ya hallara daruruwan baki daga kasashe da yankuna fiye da 100, da kuma kungiyoyin kasa da kasa. Mahalarta taron sun amince cewa, demokuradiyya wani abu ne mai muhimmanci ga daukacin bil-Adama, kuma akwai abubuwa da dama dake tabbatar da demokuradiyya. Bello Wang na dauke da cikakken bayani.