logo

HAUSA

IOC: hukumar Ifs da hukumomin wasannin Olympics na nahiyoyi biyar sun nuna goyon baya ga ‘yan wasan Rasha da Belarus da su koma gasannin kasa da kasa

2023-04-07 10:18:36 CMG Hausa

Kwamitin shirya wasannin Olympics na kasa da kasa wato IOC ya bayyana a kwanakin baya cewa, hukumar hadin gwiwar wasannin motsa jiki ta duniya wato Ifs da hukumomin wasannin Olympics na nahiyoyi biyar dukkansu sun nuna goyon baya ga ‘yan wasan kasar Rasha da na kasar Belarus su koma gasannin kasa da kasa a matsayin daidaikun yan wasa yan ba ruwan mu.

Bayan da aka gudanar da taro na kwana na uku na kwamitin gudanarwar IOC, shugaban kwamitin IOC Thomas Bach ya sake amsa tambayoyi daga ‘yan jarida ta yanar gizo. Daga baya kuma, kwamitin IOC ya bayar da sanarwa ta shafin internet cewa, game da shawarar da kwamitin gudanarwar IOC ya bayar wato amincewa da ‘yan wasan kasar Rasha da na kasar Belarus da su koma gasannin kasa da kasa a matsayin daidaikun yan wasa yan ba ruwan mu, hukumar hadin gwiwar wasannin motsa jiki ta duniya wato Ifs da hukumomin wasannin Olympics na nahiyoyi biyar, wadanda suka wakilci kasashe da yankuna 206 na duniya, dukkansu sun nuna goyon baya gare ta.

Bayan da kwamitin gudanarwar IOC ya gudanar da wani taro a birnin Lausanne dake kasar Switzerland. Hukumar IOC ta bayar da shawarwari guda shida game da amincewa ‘yan wasan kasar Rasha da na kasar Belarus da su koma gasannin kasa da kasa a matsayin daidaikun yan wasa yan ba ruwan mu, ciki har da matsayinsu, da bin ka’idojin yaki da magani kara kuzari da sauransu.

Hukumar IOC ta yi bayani game da dalilin da yasa aka bayar da wannan shawara. Wani mai binciken musamman na majalisar kula da hakkin dan Adam ta MDD ya bayyana a ranar 1 ga watan Febrairu na shekarar bana cewa, masanan MDD sun yabawa kwamitin IOC domin yayi la’akari da amincewa da ‘yan wasan kasar Rasha da na kasar Belarus da su koma gasannin kasa da kasa a matsayin daidaikun yan wasa yan ba ruwan mu, sun bayyana cewa, sun kalubalanci kwamitin IOC da cimma irin shawara, da tabbatar da daina nuna bambanci ga duk ‘yan wasa domin asalinsu.

Kwamitin IOC ya bayyana cewa, kasa da kasa su ma sun nuna goyon baya ga tunanin wasannin Olympics. A ranar 1 ga watan Disamba na shekarar bara, babban taron MDD ya zartas da kuduri mai taken “wasanni ya kasance wani bangaren dake sa kaimi ga samun bunkasuwa mai dorewa”, inda aka yi nuni da cewa, ya kamata a gudanar da manyan gasannin kasa da kasa bisa tunanin zaman lafiya, da fahimtar juna, da hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, da sada zumunta, da amincewa da bambance-bambance a tsakanin kasa da kasa, kana a girmama irin gasannin mai sa kaimi ga yin hadin kai da samun sulhu da juna.

Kudurin ya kara da cewa, a tabbatar da kundin tsarin mulkin wasannin Olympics, kana a tabbatar da kin amincewa da duk wane irin aikin nuna bambance-bambance a yayin wasannin Olympics. Kwamitin IOC ya bayyana cewa, dukkan kasashe membobin MDD sun amince da kudurin ciki har da kasar Ukraine da kasar Rasha.

Bisa irin yanayin, kwamitin IOC yana kokarin neman hanyar amincewa ‘yan wasan kasar Rasha da na kasar Belarus da su koma gasannin kasa da kasa a matsayin daidaikun yan wasa yan ba ruwan mu.

 

Kungiyar wasan kwallon kafa ta Barcelona tana kokarin neman zama zakara a gasar La Liga

 

A kwanakin baya, shugaban kungiyar wasan kwallon kafa ta Barcelona ta kasar Spaniya Joan Laporta ya bayyana wa dan jarida a birnin Warsaw dake kasar Poland cewa, kungiyarsa ta Barcelona tana kokarin neman zama zakara a gasar La Liga, amma har yanzu ba a gama wasan ba, akwai ayyuka da dama da ake bukatar gudanar da su.

Zuwa yanzu, kungiyar wasan kwallon kafa ta Barcelona ta samu nasara sau 22 da kunnen doki 2 da kuma cin tura 2, ta samu maki 68, inda ta zama matsayin farko a jerin sunayen kungiyoyin wasan dake halartar gasar La Liga, kuma kungiyar Real Madrid ta zama matsayi na biyu, akwai gibin maki 12 a tsakaninsu. Akwai sauran zagaye 12 kafin gama La Liga a wannan kaka.

Shugaban kungiyar Barcelona Laporta ya bayyana cewa, kungiyarsa tana da kwarewa ko a fannin tsaron gida ko kai hari a wasa. Amma akwai sauran lokaci wato watanni fiye da biyu kafin gama gasar La Liga a wannan kaka, ba a gama fafatawa a gasar ba, don haka, bai kamata a fara taya murnar zama zakara ba, tilas ne dukkan membobin kungiyarsa su ci gaba da yin kokari.

Mashahurin dan wasan gaba na kasar Poland Robert Lewandowski ya buga wasa mai kyau a kakar farko bayan ya shiga kungiyar Barcelona, Lewandowski mai shekaru 34 da haihuwa ya ci kwallaye 15, zuwa yanzu shi ne a matsayin farko na dan wasan da ya fi zura kwallaye a raga a gasar La Liga ta wannan kaka.

Malam Laporta ya bayyana cewa, yana farin ciki sosai da kawo dan wasa Lewandowski a cikin kungiyar Barcelona, shigowarsa a cikin kungiyar ta taimakawa mata a yayin wasan sosai, domin shi dan wasa ne mai kwarewa, kana halayensa na da kyau sosai yayin wasan da ya buga. Ya kara da cewa, sauran ‘yan wasan gaba na kungiyar su kan maida hankali ga yadda za a zura kwallaye a cikin raga, amma Lewandowski ya fi son samar da gudummawa ga duk kungiyar a fannoni daban daban, kamar taimakawa ‘yan wasa matasa wajen samun ci gaba.

Hakazalika kuma, malam Laporta ya ce, za a kara baiwa Lewandowski goyon baya. Yayin wasan dake tsakanin kungiyar Barcelona da kungiyar Real Madrid, Lewandowski ya fi samun dama, amma bai rike damar ba. Amma ya samar da gudummawa sosai ga kungiyar, Laporta ya bayyana godiya sosai gare shi. A ganin Laporta, bayan Lewandowski ya shiga kungiyar Barcelona, ya samu kwarewa sosai a fannoni daban daban.(Zainab Zhang)