logo

HAUSA

Kamata ya yi a hadin kai don magance kwayar cuta ta COVID-19

2023-03-25 18:56:10 CMG HAUSA

 

Abokai, masana kimiyya da dama na kokarin gano asalin kwayar cutar COVID-19, don fahimtar hanyar da ta bi ta yaduwa, ta yadda za a magance cututtuka da kwayar Corona ta haifar.

Tun daga shekarar 2020, shugaban kwalejin nazarin harkokin kiwon lafiya na kasar Amurka Francis Collins ya wallafa wani bayani mai taken “Nazarin da aka yi ya shaida cewa : kwayar COVID-19 ya samun asali daga indallahi”, inda bayanin ya ruwaito da kuma goyon bayan sakamakon nazarin da wani rukunin nazari na kasa da kasa dake karkashin kwalejin ya yi, inda mambobin rukunin suka kwatanta kwayoyin Corona iri daban-daban ciki hadda kwayar dake haifar da cutar COVID-19, sun kai ga matsaya daya cewa: wannan kwayar cuta ta samu asali daga indallahi.

Nazarin da dimbin masana suka yi na nuna cewa, akwai kwayoyin Corona a jikin wasu dabobbin daji ciki hadda jemage da pangolin, kila kwayoyin za su yaduwa daga jikinsu zuwa Bil Adama. Barkewar cutar COVID-19 a wannan karo na yi gargadi ga Bil Adam cewa: dole ne mu yi iyakacin kokarin gano yadda kwayoyin Corona ke yaduwa daga jikin dabbobin daji zuwa jikin Bil Adama, kuma hakan ba kawai zai ba da taimako wajen magance COVID-19 da muke fuskanta, har ma zai taka rawa wajen magance cututukan da kwayoyin Corona za su haifar.

Masana kimiyya na kokarin yin nazari da fadakar da jama’a sakamakon da suka samu, kamata ya yi kasashe daban-daban su hada kansu don magance cututtuka da mai yiwuwa ne sabbin kwayoyin Corona za su kawo mana. Wasu ‘yan siyasa dake yunkurin siyasantar da aikin gano asalin cutar shin ko ba su kula da rayukan fararen hula ba? (Mai zana kuma rubuta: MINA)