logo

HAUSA

Nazarin Kwayoyin Cuta Da Amurka Take Yi Yana Kawowa Duniya Illa

2023-03-18 18:48:44 CMG HAUSA

DAGA MINA

  Abokai, nazarin kwayoyin cuta da Amurka take yi a duniya ya dade yana haifar da kalubaloli irin daban-daban. Ciki hadda nazari kan Bil Adama a boye da nazari wasu kwayoyin cuta mafi kamuwa da Bil Adama, har ma da bacewar wasu kwayoyin cuta da sauransu, duk sun kawo babbar illa ga jama’a, inda suka jefa kasashe daban-daban cikin mawuyancin hali na rashin tsaro.

Ran 24 ga watan Fabrairun bara, an tada rikici tsakanin Rasha da Ukraine, inda aka fara tattaunawa kan irin wannan nazari da Amurka take yi a boye a kasashe daban-daban a duniya. Game da wannan batu, kasashe da dama sun nuna shakku da damuwarsu, amma Amurka ta yi kunnen uwar shegu. Har zuwa yanzu, akwai shaddu dake bayyana cewa, nazarin da Amurka take yi a kasashen waje, na fakewa da batun ba da tallafin jiyya ga ketare, na da alaka da ayyukan soja. Wadannan dakunan nazarin da Amurka ta kafa a kasashen duniya, za su kawo babbar illa ga kasashe daban-daban da na al’ummominsu

To, a matsayinta na kasar dake kiran kanta a matsayin “Fitila a fannin hakkin Bil Adama”, yaushe ne za ta ba da bayani kan wadannan ayyukan da take yi a sassan duniya?(Mai zana da mai rubuta: MINA)