Ahmad Adamu Umar: Ina son inganta tsaron intanet a Najeriya bisa ilimin da na karo a China
2023-04-04 15:48:04 CMG Hausa
Ahmad Adamu Umar, dan Najeriya ne wanda aka fi sani da Khalifa Ado Namagaji Kazaure, a yanzu haka yana karatun digiri na biyu a fannin tsaron yanar gizo ta Intanet a jami’ar kimiyya da fasahohin laturoni ko kuma UESTC a takaice dake birnin Chengdu na lardin Sichuan na kasar Sin.
A hirar da ya yi da Murtala Zhang, Malam Ahmad ya bayyana dalilin da ya sa ya kudiri aniyar zurfafa karatu a kasar Sin, da yadda za’a iya inganta hadin-gwiwa da mu’amala tsakanin Najeriya da kasar Sin a fannin tsaron intanet. A karshe, ya kuma bayar da kyawawan shawarwari ga ‘yan Najeriya, musamman matasan da suke son yin karatu a kasar Sin. (Murtala Zhang)