Ta yaya aka samu nasarar kiyaye rayuka da lafiyar al’ummar Sinawa daga cutar COVID-19?
2023-04-04 08:31:04 CMG Hausa
Shekaru 3 ke nan bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a duniya. A cikin wadannan shekaru 3 da suka gabata, ko da yaushe kasar Sin tana mayar da jama’arta da rayukansu a gaban komai. Ta kyautata matakan yaki da cutar bisa lokaci da yanayin da ake ciki, da daidaita aikin raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasa, da na dakile yaduwar cutar yadda ya kamata. Lamarin da ya sa aka magance yaduwar nau’o’in kwayoyin cutar masu haddasa saurin mutuwa a kasar, tare da kiyaye rayuka da lafiyar jama’arta yadda ya kamata.
Tun daga watan Nuwamban shekarar 2022 da ta gabata, kasar Sin ta rika kyautata matakan yaki da cutar, bisa manufar “kiyaye lafiya da magance samun yawan wadanda ke fama da cutar mai tsanani”, ta kuma samu nasara cikin kankanin lokaci, inda aka yi wa mutane fiye da miliyan 200 jinya, tare da ceton wadanda ke fama da cutar mai tsanani kimanin dubu 800. Lamarin da ya sa yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar ya fi kankanta a duk duniya. Kasar Sin ta samu gagarumar nasarar yaki da cutar ta COVID-19, tare da yin abin al’ajabi a tarihin dan Adam.
Cutar COVID-19 wata nau’in cuta ce mai yaduwa a duk duniya, wanda ba safai a kan ga irin ta a tarihin dan Adam ba. Haka kuma, ita ce matsalar kiwon lafiyar jama’a mafi tsanani da duk duniya ta fuskanta, tun bayan babban yakin duniya na biyu. Don haka aikin yaki da cutar ya kasance wata babbar jarrabawa ga ko wace kasa, ciki har da kasar Sin.
Sanin kowa ne cewa, kasar Sin na da al’umma mai yawan gaske, har ma yawan al’ummar ta ya kai biliyan 1.4. Kana yawan mazauna gari guda a cikin kasar sun wuce yawan al’ummun wata karamar kasa baki daya. A manyan birane kamar su Beijing, da Shanghai da dai sauransu, an fi samu yawan mutane, da kuma yawan sa’o’in cudanyar mutane daga wurare daban daban. A yankunan karkara da wasu kananan garuruwanta kuma, ba a samun kyakkyawan yanayin kiwon lafiya sosai, kuma yawan ma’aikatan jinya da na muhimman kayayyakin more rayuwa ta fuskar kiwon lafiya, da ma na na’urorin ceton masu fama da cutar mai tsanani, ba su kai na kasashe masu sukuni ba. Don haka an fi samun wahalhalu wajen dakilewa, da kandangarkin cutar, da ma ba da jinya ga masu fama da cutar. Ko da yake tana fuskantar wadannan matsaloli, amma duk da haka kasar Sin ta yi iyakacin kokarinta wajen yaki da cutar.
Daga karshen shekarar 2019, zuwa watanni 6 na farkon shekarar 2020, kasar Sin ta gano barkewar annobar a kan lokaci, inda ta tsai da kuduri mai muhimmanci, na daukar matakin kulle a birnin Wuhan, ba tare da bata lokaci ba, lamarin da ya hana yaduwar cutar zuwa sauran sassan kasar, ta yadda Sin ta tabbatar da daidaiton dakilewa, da kandagarkin cutar a duk fadin kasar, da yin iyakacin kokarin rage asarar rayukan jama’arta. Bisa kokarin kasar Sin, ta samu nasarar magance yaduwar nau’in kwayoyin cutar COVID-19 na asali, da nau’in DELTA, lamarin da ya sa aka samu raguwar yawan masu kamuwa da cutar mai tsanani, da adadin wadanda ta hallaka.
Ban da wannan kuma, da zarar an gano kwayoyin cutar, kasar Sin ta na gabatar wa hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO hakan, ba tare da bata lokaci ko kadan ba, da bayar da tsarin kwayoyin cutar ga duk duniya ba tare da bata lokaci ba, da bayar da dabarun jinya, da dakilewa, da kandagarkin cutar ba tare da bata lokaci ba, lamarin da ya samar da labaran kimiyya ga kasashen duniya, wajen dakile yaduwar cutar, da nazarin allurar cutar da kayan gwajin cutar.
Daga watanni 6 na farkon shekarar 2020 zuwa karshen shekarar 2022, yayin da kasar Sin take kokarin hana yaduwar cutar, ta himmatu wajen nazarin magunguna da allurar rigakafin cutar. Kana ta yi wa al’ummarta mafi yawa a duniya allurar kyauta cikin gajeren lokaci, lamarin da ya sa yawan masu kamuwa da cutar, da kuma yawan mutuwar mutane sakamakon cutar dukkansu suka fi kankanta a duniya. Ta haka kasar Sin ta ba da kariya ga rayuka da lafiyar jama’arta, da kuma tabbatar da gudanar da harkokin tattalin arziki da zaman al’umma yadda ya kamata.
Bisa kididdigar da WHO ta yi, an ce, a cikin shekarar 2020 da ta 2021, yawan mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar ya kai kusan miliyan 15 a duk fadin duniya. A matsayinta na wata babbar kasa mai yawan al’umma, yadda kasar Sin ta yi kokarin dakilewa, da kandagarkin cutar, ya ceci rayuka fiye da miliyan daya, wadda ta bayar da babbar gudummawa wajen samun nasarar yaki da cutar.
Hakika dai, ba a iya raba yadda kasar Sin ta samu babbar nasarar yaki da cutar da hadin kan al’ummar Sinawa, da kwarewar ma’aikatan jinya, da matukar kokarin ma’aikatan sassan daban daban, wajen tabbatar da samar da marufin hanci da baki, da rigunan rigakafi, da dai sauran kayayyaki yadda ya kamata, har ma da kokarin masu aikewa da sakwanni ba tare da tsoron lafiyar kansu ba.
A yayin da kasar Sin take daidaita matsaloli da dama, har kullum tana mara wa kasashen duniya baya wajen yaki da cutar COVID-19. Ta samar wa kasashe 153, da kungiyoyin kasa da kasa 15, daruruwan biliyoyin kayayyakin kandagarkin cutar. Ta kuma samar wa kasashe da yankuna fiye da 180, da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 10 fasahohin dakilewa, da kandagarkin cutar, da na ba da jinya da kiwon lafiya. Kana kuma, kasar Sin ta tura kungiyoyin masana ilimin lafiya 37 zuwa kasashe 34, a kokarin samar da kyawawan fasahohinta na yaki da cutar ba tare da rufa-rufa ba. Har ila yau, kasar Sin ta samar wa kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 120 alluran rigakafin cutar fiye da biliyan 2.2, hakan ya sa kasar Sin zama kasar da ta fi samar wa kasashen duniya alluran.
Kasashe daban daban sun nuna godiyar ga kasar Sin, ciki har da Najeriya. Ministan kiwon lafiyar Najeriya Osagie Ehanire ya taba bayyana cewa, tun bayan barkewar cutar COVID-19, kasar Sin ta samar wa Najeriya kayayyakin jinya, da more fasahohin ba da jinya, kana kasar Sin ta kasance daya daga cikin kasashen da suka fi saurin ba da taimako ga Najeriya.
A fannin tattalin arziki kuwa, Sin ta raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma, yayin da take tinkarar cutar ta COVID-19, wadda ta kasance kasa dake kan gaba wajen farfardo da tattalin arzikin duniya. A shekarar 2020, kasar Sin ta zama ta farko wajen samun karuwar tattalin arziki a duk fadin duniya. A shekarar 2021 kuma, saurin karuwar tattalin arzikinta yana kan gaba a duk duniya. A shekarar 2022 kuma, jimillar tattalin arzikinta ya zarce kudin Sin yuan triliyan 120, kuma saurin karuwarsa ya kai kashi 3 cikin dari bisa na makamancin lokaci na shekarar 2021.
Bugu da kari kuma, a cikin shekarun 3, yayin da ake tinkarar yaduwar cutar, da ra’ayin kashin kai, da na ba da kariyar cinikayya, Sin ta kara bude kofarta ga kasashen waje, lamarin da ya tabbatar da samar da kayayyaki ga duniya yadda ya kamata. Jimillar kudaden kayayyakin shige da fice da kasar Sin ta samu ya zarce Yuan tiriliyan 40 a shekarar 2022, wato kwatankwacin karuwar kaso 7.7 cikin dari, bisa na makamancin lokaci na 2021.
Sakamakon kyautatuwar yanayin yaki da cutar COVID-19 da kasar Sin ke fuskanta, kasar Sin ta tsai da kudurin mayar da cutar zuwa rukunin B na cututtuka masu yaduwa, tare da daukar jerin matakai, a kokarin raya tattalin arzikinta, da maido da zaman al’ummar Sinawa na yau da kullum. Kamar yadda sabon firaministan kasar Sin Li Qiang ya bayyana, a gun taron manema labarai da aka shirya, a yayin taron shekara shekara na majalissar wakilan jama’ar Sin. Li Qiang ya ce, har yanzu cutar COVID-19 na ci gaba da yaduwa a dukkanin fadin duniya, kuma kasar Sin za ta ci gaba da mai da hankali a kanta, da tsara matakai masu dace da yanayin da ake ciki, da kara inganta tsarin kiwon lafiya, da gaggauta nazarin allurar rigakafin cutar da magungunun ta, da ma kara hadin gwiwa tare da kasashe daban daban, a kokarin kiyaye lafiya da muradun al’ummun duniya tare. (Kande Gao)