logo

HAUSA

Kasashen Afrika sun ce wa kasar Amurka “Babu ruwanki”

2023-04-03 21:32:44 CMG Hausa

Abokai na, kun fahimci damuwar iyayen yara kuwa? Wato yadda suke damuwa kan wasu abubuwan da yaransu ke yi, kamar son wasa maimakon yin karatu, da yawan mu’amala da wayar salula, da dai sauransu, abin da kan sa su zagin yara. Wannan damuwa ce da za a iya fahimta. Sai dai abin mamaki shi ne, wasu kasashe ma su kan nuna wannan nau’in damuwa na iyaye. Wato su kan kalli kansu tamkar “iyayen” sauran kasashe, inda suke son tsoma baki a harkokin cikin gida na sauran kasashen.

Misali, lokacin da Kamala Harris, mataimakiyar shugaban kasar Amurka, take ziyara a kasar Ghana a kwanakin baya, ta matsawa bangaren Ghana lamba kan batun kare hakkin ‘yan luwadi. Dalilin da ya sa haka, shi ne domin majalisar dokokin kasar Ghana na tattaunawa kan daftarin dokar haramta masu neman jinsi daya. Dangane da wannan batu, Harris ta nuna goyon baya ga‘yan luwadi, inda ta ce, “ A ganin kasar Amurka, batun kare hakkin‘yan luwadi, wani batu ne da ya shafi hakkin dan Adam, don haka kasarmu ba za ta taba ja da baya ba.”

Mun san kasar Amurka ta saba da yin katsalandan cikin harkokin gida na sauran kasashe, har ma da daukar matakan soja kan sauran kasashe, ta hanyar fakewa da kalmar “kare hakkin dan Adam”. Saboda haka kasar ba ta ganin wani kuskure a maganar Madam Harris. Sai dai kalaman nata ya fusata ‘yan kasar Ghana, inda Alban Bagbin, shugaban majalisar dokokin kasar Ghana, ya ce ba zaitaba yarda da maganar Madam Harris ba. A cewarsa, kasar Amurka na neman baiwa kasar Ghana umarni ne, lamarin da ya sabawa ruhi na Demokuradiyya.

Sa’an nan wani batu na daban da ya sa kasar Amurka damuwa shi ne huldar dake tsakanin kasashen Afrika da kasar ta Sin. Ko da yake, Kamala Harris ta ce ziyararta a nahiyar Afrika ba ta shafi kasar Sin ba. Amma rahotannin da kafofin watsa labaru na kasar Amurka suka gabatar sun nuna wata damuwa mai tsanani kan tasirin kasar Sin a kasashen Afirka. Inda kamfanin dillancin labaru na AP ya ce, lokacin da Madam Harris ke ziyara a kasar Zambia, jirgin samanta ya sauka a wani filin jirgin sama da wani kamfanin kasar Sin ya yi masa kwaskwarima, bisa rancen kudin da kasar Sin ta bayar. A nata bangare, jaridar The New York Times, ta ce ayarin motocin Harris ya wuce wata babbar mararrabar hanya dake tsakiyar birnin Accra na kasar Ghana, inda aka rubuta a wani kwali cewa, kasar Sin ce ta ba da tallafin kudin gina mararrabar hanyar. A cewar kamfanin AP, huldar kut-da-kut dake tsakanin Afrika da Sin ta sa gwamnatin kasar Amurka damuwa sosai, saboda tana tsoron ganin yadda kasashen Afirka suka kara karkata ga bangaren kasar Sin.

Wannan damuwa mai tsanani da kasar Amurka ta nuna ya ja hankali shugaba Nana Akufo-Addo na kasar Ghana, don haka ya mayar da martani. Yayin wani taron manema labaru, kuma a gaban Madam Kamala Harris, shugaban na kasar Ghana ya ce, “ Watakila kasar Amurka za ta damu game da tasirin kasar Sin a nahiyar Afrika, amma mu ba ma damuwa. Kasar Sin tana cikin dimbin kasashen da kasar Ghana ke hulda da su, ma iya cewa dukkan kasashen duniya abokanmu ne.” Ma’ana “Akwai dimbin kasashe a duniyarmu, kuma za mu iya hulda da duk wanda muke son hulda. Wannan batu ba ruwan kasar Amurka a ciki. ”

Bayan haka, Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasar Najeriya, shi ma ya wallafa wani bayani a shafinsa na sada zumunta na Twitter, inda ya ce, “Galibin kasashen Afrika ba za su nemi a yi musu afuwa bisa huldar kut-da-kut dake tsakaninsu da kasar Sin ba. Saboda kasar Sin ta gabatar da kanta a wurare da lokutan da su kasashen yamma ba su son kasancewa ciki. Kasashen Afrika na bukatar rancen kudi, da kayayyakin more rayuwa, sa’an nan kasar Sin ta biya musu bukatunsu.”

Gaskiya kasar Amurka ta sha nuna damuwa, inda ta damu da yiwuwar abkuwar“keta hakkin dan Adam” a kasashen Afrika, da yadda suke hulda da kasar Sin, da sauran batutuwa daban daban. Sai dai kasashen Afrika sun riga sun bayyana mata cewa, “Babu ruwanki ko kadan!"Wai mai Daki shi ya san inda yake masa Yoyo. (Bello Wang)