logo

HAUSA

Xiong'an na da burin zama biranen nan gaba masu inganci abin koyi

2023-04-02 19:16:18 CRI

  Sabon yankin Xiong'an, wani sabon birni mai fadin murabba'in kilomita 1,770 da ake ginawa a lardin Hebei dake yankin arewacin kasar Sin, yana da burin zama wani yanki mai kiyaye muhalli, da karancin iskar carbon kuma kyakkyawan tsari na birane abin koyi a nan gaba

An dai kafa yankin Xiong'an mai tazarar kilomita 100 a kudu maso yammacin birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin ne a watan Afrilun shekarar 2017, a matsayin wani sabon yankin raya tattalin arziki kana wata babbar cibiyar bunkasuwa a babban yankin Beijing-Tianjin-Hebei.

A cikin shekaru 6 da suka gabata, an zuba tsabar kudi fiye da dalar Amurka biliyan 74 a muhimman ayyuka 240 a yankin.

Bisa yadda hukuma ta tsara, ana ganin yankin Xiongan yana bunkasa zuwa birni na zamani, da jama’a za su ji dadin zaman rayuwa nan da shekarar 2035. (Ibrahim)