logo

HAUSA

Chelsea Ta Shiga Zawarcin Victor Osimhen

2023-03-18 16:07:03 CRI

NUEFA Za Ta Biya Magoya Bayan Liverpool Kudin Tikitin Su

 

Hakan ya biyo bayan wani kwamiti mai zaman kansa da ya binciko cewar UEFA ce ta haddasa turmutsitsin da ya faru, kafin wasan karshe tsakanin kungiyar Liverpool da Real Madrid.

Magoya baya da dama ba su samu damar shiga kallon wasan ba, an kuma bada barkonon tsohuwa a fafatawar da aka yi lattin minti 36 kafin fara wasan saboda matsalar da aka samu.

UEFA ta ce za ta biya dukkan tikiti dubu 19, 618 da aka bai wa magoya bayan Liverpool, domin kallon fafatawar da aka yi a Faransa kuma wasu rahotanni sun bayyana cewa tuni aka fara biyan magoya bayan.

Real Madrid ce ta ci Liverpool 1-0 ta dauki Champions League na 14 jimilla kuma a kakar nan kungiyoyin sun buga a Ingila a zagayen ‘yan 16 a gasar zakarun Turai, inda Real Madrid ta ci Liverpool 5-2 a filin wasa na Anfield ranar 21 ga watan Fabrairu.

Real Madrid za ta karbi bakuncin Liverpool a wasa na biyu ranar 15 ga watan Maris a Santiago Bernabeu sai dai a wannan karon Liverpool, za ta je Sifaniya da kwarin gwiwa, bayan da ta doke Manchester United 7-0 ranar Lahadi a Premier League a Anfirld.

Ita kuwa Real Madrid, waddaa Barcelona ta bawa tazarar maki tara a teburin La Liga, ta je ta tashi 0-0 da Real Betis ranar Lahadi kuma wasa na uku kenan kungiyar ba ta samu nasara ba a jere.

 

Chelsea Ta Shiga Zawarcin Victor Osimhen

 

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta bayyana shirinta na ninka albashin da dan wasan gaba na Najeriya ke dauka a Napoli Victor Osimhen, duk da cewar kungiyoyin Manchester United da Tottenham sun nuna sha’awar daukar dan wasan.

A cewar rahotanni, Chelsea na shirin dauko dan wasan da yake taimaka wa Napoli wajen ganin ta lashe gasar Serie A a karon farko a wannan karnin, ganin yadda ya jefa kwallaye 19 daga cikin wasannin lig 21 da ya yi wa kungiyarsa a kakar wasan bana.

A yanzu Osimhen ne mutum na biyu wajen daukar albashi mafi yawa a kungiyar, inda ake biyan shi Euro miliyan biyar kwatankwacin Naira miliyan dubu biyu da miliyan dari biyar a duk shekara, amma sai dai Chelsea ta ce a shirye ta ke ta ninka wa dan wasan albashinsa.

Chelsea na fuskantar kalubale daga bangaren Manchester United da kuma Tottenham wajen zawarcin dan wasan, inda Tottenham ke ganin dan wasan a matsayin wanda zai maye mata gurbin Harry Kane.

 

 

Ana Yi Wa Graham Potter Barazanar Kisa

Kungiyar ta ci wasanni biyu daga cikin 14 da ta buga baya a dukkan fafatawa, wadda a makon jiya Southampton ta doke ta a Premier League sai dai duk da haka shugabancin kungiyar na Chelsea ya sanar cewar tana goyon bayan Potter da iyalansa dari bisa dari tana tare da shi.

”Na karbi sakon wasika ta internet, wanda ke dauke da barazanar kisa ba sakone mai dauke da kalaman farin ciki da za ka karanta ba.” A cewar Graham Potter, dan asalin kasar Ingila.

Graham Potter ya zama kociyan Chelsea cikin watan Satumban shekarar da ta gabata, bayan da ta kori Thomas Tuchel – wasa tara Chelsea ta yi nasara daga 25 baya-bayan nan.

Chelsea tana ta 10 a teburi da tazarar maki 11 tsakaninta da gurbin ‘yan Champions League da ke fatan buga wasannin badi sanann ranar Lahadi Chelsea ta buga wasan hamayya a gidan Tottenham a gasar Premier League mako na 25 inda ta yi rashin nasara da ci 2-0.

Ba Zan Bar Shugabancin Barcelona Ba, Cewar Laporta

Ranar Litinin Tebas ya ce ya kamata Laporta ya yi murabus idan har ya kasa fayyace wasu kudi da aka biya Jose Maria Enrikuez Negreira, tsohon shugaban kwamitin alkalan wasa a Sifaniya.

A hirar sa da manema labarai akan ko zai ajiye aikin shugabancin kungiyar, Laporta ya ce wannan hukunci ne daga wajen mambobi kan shugabansu, saboda haka sai abinda suka yanke.

An zabi Laporte da yawan rinjaye a watan Maris din shekara ta 2021 kuma zuwan sa kungiyar ya kawo gyara sosai musamman wajen siyo ‘yan wasa da kuma daukar Dabi a matsayin mai koyarwa.

Takaddama ta tashi ne ranar Larabar da ta gabata kan biyan fam miliyan 1.2 ga kamfanin Negreira tsakanin 2016 zuwa 2018 sannan daga baya aka bankado cewar kungiyar ta biya mai shekara 77 kudi yuro miliyon 7 tsakanin shekarar 2001 zuwa 2018, shekarar da ya bar mukamin shugaban kwamitin alkalan wasa na Sipaniya.

Barcelona wadda rabonta da La Liga tun bayan kakar wasa hudu tana ta daya a teburin bana da tazarar maki takwas tsakanin ta da Real Madrid ta biyu sai dai wasu na shakku kan kwazon Barcelona ko makomarta kan wannan batun da ta musanta.