Boao: Kasar Sin Ta Karfafa Gwiwar Kasa Da Kasa
2023-03-31 21:48:20 CMG Hausa
Taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar Asiya na Boao da aka gudanar daga ranar 28 zuwa 31 ga wata ya samu mahalarta fiye da 1500 daga sassan siyasa, masana’antu da kasuwanci da masana daga kasashe da yankuna fiye da 50 na nahiyoyi guda 5. Yayin da ake fuskantar rashin tabbas da rashin kwanciyar hankali a duniya, taken babban taron na bana shi ne “duniya mai rashin tabbas: yin hadin gwiwa da hadin kai domin daidaita kalubale da kuma bude kofa don kara azama kan samun ci gaba da ke shafar kowa”, wanda ya kasance take mai ma’ana sosai, da ya bayyana burin mutane na samun tabbas.
A kwanaki 4 da suka wuce, baki mahalartar taron da dama sun bayyana ra’ayoyinsu kan kasar Sin a yayin da suke hira da ‘yan jarida, alal misali, kasar Sin ta bayyana wa duniya aniyarta ta bude kofa ga ketare. Kasar Sin ta kiyaye ci gaban tattalin arzikinta. Kasuwannin sayayya a kasar Sin na da matukar muhimmanci ga ragowar kasashen duniya. Kalamansu sun nuna cewa, sun ji dadin halartar taron a kasar Sin, sun kuma nuna kwarin gwiwa kan kasar Sin mai tabbas. Ta yaya suka samu irin wannan kwarin gwiwa?
Yayin da bakin suke zantawa da ‘yan jarida, sun yaba da kasar Sin a fannonin kasuwanni mai cike da kuzari, kyaun yanayin kasuwanci da cikakken tsarin samar da kaya. Suna da yakini kan kasuwannin kasar Sin.
Haka kuma sun nuna kwarin gwiwa kan yadda kasar Sin take tsayawa kan bude kofa ga ketare. Daga taron tattaunawa tsakanin manyan jami’ai kan ci gaban duniya zuwa taron dandalin tattaunawar Asiya na Boao, kasar Sin tana ta bayyana wa duniya cewa, duk sauye-sauyen da za a samu a duniya, kasar Sin za ta ci gaba da yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare da kuma yin kirkire-kirkire don samun ci gaba. (Tasallah Yuan)