logo

HAUSA

UNECA ta kaddamar da shirin zamanantar da tsarin tattara alkaluman kididdga a Afrika

2023-03-30 10:08:40 CMG Hausa

Hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD (UNECA), ta kaddamar da wani shiri domin taimakawa kasashen Afrika, wajen zamanantar da yadda ake tattara alkaluman kididdiga domin harkokin gwamnati.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce shirin ya bi “Tsarin sauyi da zamanantar da kididdiga da ake amfani da ita a hukumance a Afrika na shekarar 2023 zuwa 2030”, wanda taron ministocin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki na hukumar UNECA ya amince da shi a makon da ya gabata.

Sanarwar ta ce alkaluman da cibiyoyin gwamnati suka tattara, na bayar da bayanai masu inganci a bangarori daban-daban, wadanda ke da muhimmanci ga burikan samun ci gaba mai dorewa bisa ra’ayin ganin ba a bar kowa a baya ba, da rage kudin da ake kashewa wajen tattara bayanai domin ayyukan gwamnati da rage matsi kan wadanda suke bayar da amsa.

Yanzu haka ana gudanar da taruka biyu a kasashen Kamaru da Uganda, domin kaddamar da tsarin a matsayin wani bangare na sabon shirin. (Fa’iza Mustapha)