logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya yi jawabi a Boao

2023-03-30 21:18:07 CMG Hausa

Yau Alhamis 30 ga wata ne, aka yi bikin bude taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar harkokin Asiya na Boao na bana a garin Boao na lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin. A gun bikin, firaministan kasar Sin Li Qiang, ya gabatar da wani muhimmin jawabi, inda ya bayyana cewa, cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta samu jerin muhimman sakamako a kokarinta na gina al’umma mai makoma ta bai daya ga daukacin bil adama.